Biyubabu: Lawan Da Akpabio Ba Sa Cikin Yan Takarar Senata, INEC
- Hukumar Zabe INEC ta ce ba ta amince da saka sunan Sanata Ahmed Lawan da Godswill Akpabio a matsayin yan takarar senata a yankunan su ba
- Hukumar INEC ta ce zata yi amfani da kwafin fom din sunaye yan takara da jam'iyyu suka gabatar mata kafin ta rufe dandalin tantance sunaye
- Form EC9 shine fom din sunayen yan takara da jam’iyyun siyasa ta mika wa INEC kuma sune a tashar INEC
Abuja - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ce ba ta amince da saka sunan Sanata Ahmed Lawan matsayin ‘yan takarar senata a Yobe ta Arewa da Godswill Akpabio a matsayin dan takarar senata a Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma ba. Rahoton LEADERSHIP
Hukumar INEC ta ce bata dauki daya daga cikin mutanen biyu a matsayin yan takarar Sanata a zaben 2023 mai zuwa ba.
Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata mai taken: ‘zarge-zarge dangane da tantance ‘yan takara a wasu gundumomin sanatoci da aka gabatar wa ‘yan jarida.
Okoye ya ce a matsayin shaida na rawar da Hukumar ta taka, tun da farko an gabatar da kwafin gaskiya na Form 9C da jam’iyyun suka shigar kuma Hukumar ta samu a ranar 17 ga Yuni, 2022 lokacin da aka rufe dandalin tantance sunaye.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Domin a fayyace, ya ce Form EC9 shine fom din sunayen yan takara da jam’iyyun siyasa ta mika wa INEC kuma sune a tashar ta INEC.
Ya ce an yi nuni a fili a kan sunan fom din da aka karba a ranar 17 ga watan Yuni, 2022 lokacin da aka rufe tashar.
Dalibin Makarantar Sakandare Ya Kera Na'urar Mutum Mutumi Da Kansa A Jihar Kano
A wani labari kuma, Isah Barde, matashi dan shekara 17 da ya kammala karatunsa na sakandare a jihar Kano, ya kera Na'urar Mutum Mutumi daga tarkace, inda ya yi amfani da kwali, bututu, ledodi, moto, aluminum, da dai sauransu, a matsayin kayan aikin sa. rahoton Daily Trust
Isah yayi nazarin karantar fasahar kere-kere da zama kwararre a harkar leken asiri, duk da matsalar kudi da ke gabansa.
Asali: Legit.ng