Rikicin PDP: BoT Sun Kafa Kwamitin Sulhu Da Zai Gana Da Wike, Fusatattun Mambobi

Rikicin PDP: BoT Sun Kafa Kwamitin Sulhu Da Zai Gana Da Wike, Fusatattun Mambobi

  • Mambobin BoT na jam'iyyar PDP sun yunkuro da wani babban shiri da nufin kawo karshen rikicin cikin gida da ya addabi jam'iyyar
  • A taron da suka gudanar yau Laraba, BoT sun kafa sabon kwamitin da suka ɗora wa alhakin rarrashin mambobi irin su Wike da suka fusata
  • Gwamna Wike ya nuna rashin jin daɗinsa tun bayan zaɓen fidda gwani da zaɓen mataimaki, ya gindaya sharudɗa

Abuja - Kwamitin amintattu BoT na jam'iyyar PDP ya kafa sabon kwamitin da zai shiga tsakani don rarrashin Mambobin jam'iyyar da suka fusata, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Wasu daga cikin mambobin da suka fusata waɗan da ake fatan Kwamitin zai rarrashe su sun haɗa da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da sauran jiga-jigan PDP da ke goyon bayansa.

Kara karanta wannan

Bidiyon mace mai nishadantarwa sanye da hijabi a wani chasu ya janyo maganganu

Gwamna Wike da Atiku.
Rikicin PDP: BoT Sun Kafa Kwamitin Sulhu Da Zai Gana Da Wike, Fusatattun Mambobi Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shugaban BoT, Walid Jibrin, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba jim kaɗan bayan fitowa daga taron mambobin kwamitin wanda ya shafe sama da awanni biyu.

"Sabon kwamitin zai kasance kwamiti ne na kowa da kowa," inji shi. Hakan na nufin baki ɗaya mambobin BoT suna cikin kwamitin sulhun.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabinsa ya ce:

"Mun kafa daga cikin kwamitin BoT wani sabon kwamiti wanda zai shiga tsakanin ɓangarorin da ke fushi da juna musamman tsakanin Atiku Abubakar da gwamna Wike da duk wani rikici a faɗin kasar nan cikin jam'iyyar mu."

Shin yaushe kwamitin zai kammala aikinsa?

Sai dai Mista Jibrin bai bayyana a jawabinsa iya adadin lokacin da kwamitin zai ɗauka wajen shawo kan fusatattun jiga-jigan jam'iyyar PDP ba.

"Ba zan iya faɗa muku ga iya lokacin ba Amma a halin yanzu zamu nufi gidan ɗan takara ne da ke Asokoro domin fara aiki."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: NBC Ta Ci Aminiya Tarar Naira Miliyan 5 Saboda Bidiyon Tona Asirin Yan Bindiga

A wani labarin kuma Ɗan Majalisar Tarayya Na Zango Biyu, Ɗan Takarar Gwamna Da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Sauya Sheka

Tsohon ɗan majalisar dokokin tarayya, Chief Linus Okorie, da wasu Jigogi a jam'iyyar hamayya PDP sun koma LP a Ebonyi.

Daga cikin masu sauya sheƙan har da wani ɗan takara da ya nemi tikitin gwamna karkashin PDP da kuma tsohon kwamishina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262