2023: Ɗan Majalisar Tarayya Na Zango Biyu Da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Koma LP

2023: Ɗan Majalisar Tarayya Na Zango Biyu Da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Koma LP

  • Tsohon ɗan majalisar dokokin tarayya, Chief Linus Okorie, da wasu jigogi a jam'iyyar hamayya PDP sun koma LP a Ebonyi
  • Daga cikin masu sauya sheƙan har da wani ɗan takara da ya nemi tikitin gwamna karkashin PDP da kuma tsohon kwamishina
  • Babbar jam'iyyar hamayya na fama da rikici a matakin ƙasa wanda ya biyo bayan zaɓen fidda gwani na takarar shugaban ƙasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ebonyi - Tsohon ɗan majalisar tarayya kuma babban ƙusa a jam'iyyar PDP, Chief Linus Okorie, tare da wasu jiga-jigan jam'iyyar guda uku sun sauya sheƙa zuwa Labour Party (LP) a jihar Ebonyi.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa sauran jiga-jigan PDP da suka ɗauki matakin sauya sheƙa zuwa LP sun haɗa da ɗan takarar gwamnan a PDP, Chief Eze Emmanuel.

Tambarin jam'iyyar Labour Party.
2023: Ɗan Majalisar Tarayya Na Zango Biyu Da Wasu Jiga-Jigan PDP Sun Koma LP Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sauran su ne, Tsohon kwamishinan ilimi a jihar Ebonyi, Prince Chibuez Agbo, da kuma wani babban ƙusa mai faɗa aji, Anselem Enigwe.

Kara karanta wannan

2023: Wasu Shugabannin PDP Masu Ci Da Dubbannin Mambobi Sun Sauya Sheƙa Zuwa APC

Legit.ng Hausa ta fahimce cewa an samu wannan cigaban ne a dai-dai lokacin da rikicin cikin gida ya dabaibaye babbar jam'iyyar hamayya a matakin ƙasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a kwanakin baya ya sha alwashin cewa zai yi duk me yuwuwa wajen rarrashin mambobin PDP da suka ɗau abun da zafi.

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, na ɗaya daga cikin waɗan da ba su ji daɗin abubuwan da suka faru a PDP ba yayin da kuma bayan zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa.

Wike, wanda ke da goyon bayan wasu gwamnoni da jiga-jigan PDP, ya ƙi bayyana goyon bayansa ga takarar Atiku, wasu bayanai a baya-bayan nan sun nuna cewa tsagin gwamnan sun kafa sharaɗin cewa shugaban PDP ya yi murabus.

Sai dai a yanzun, kwamitin amintattu BoT na jam'iyyar PDP ta ƙasa ya kira taron masu ruwa da tsaki da ya haɗa da Wike da Atiku, a wani yunkurin kawo karshen rikicin da ke faruwa.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Gwamnan Arewa Ya Bi Sahun Wasu Jiga-Jigan PDP, Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Gwamna Wike ya kafa sharaɗi

A wani labarin kuma Wike ya Zauna da Gwamnonin PDP, ya Gindaya Sharadin Marawa Atiku Baya

A ranar Lahadin nan da ta wuce, 31 ga watan Yuli 2022, Gwamnan Ribas watau Nyesom Wike ya yi zama da mutanensa da jagororin jam’iyyar PDP.

Daily Trust ta kawo rahoto cewa Mai girma Nyesom Wike ya hadu da masu ruwa da tsaki a PDP da wadanda suka yi masa yakin neman tikiti na zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262