Takarar Tinubu-Shettima: Jami’an DSS sun ankarar da Buhari abin da suka hango
- Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya zabi Musulmi, Kashim Shettima ya zama Abokin takarsa a APC
- Hukumar DSS ta na ganin hakan zai haifar da rashin zaman lafiya tsakanin Musulmai da Kiristoci
- DSS ta rubuta takarda wanda ta je hannun NSA, tana bayanin hadarin tikitin Musulmi-Musulmi
Abuja - Matsayar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dauka na tsaida Musulmi a matsayin abokin takara a zaben shugaban kasa, zai iya jawo rigima a kasa,
Rahoton da Leadership ta fitar a ranar Juma’a, ya bayyana cewa hukumar DSS ta rubutawa shugaban kasa takarda a game da shirin da APC ta ke yi a 2023.
Bayanan tsaro na sirri da hukumar farin kaya na DSS ta aikawa Mai girma shugaban kasa ya nuna daukar Musulmi da Musulmi zai iya haifar da rikicin addini.
DSS ta gabatar da binciken, kuma ta damka rahoto ga Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Janar Babagana Monguno mai ritaya domin a dauki mataki.
DSS ta nunawa Janar Babagana Monguno cewa ya kamata Bola Tinubu ya duba halin tsaro da kasa za ta samu kan ta, kafin ya dauko abokin takararsa a APC.
Jaridar nan ta Peoples Gazette ta samu ganin takardar bayan ta shiga ofishin Babagana Monguno.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wata majiya ta shaida cewa shugaban NSA ya duba rahoton, ta kuma sa shi a jerin abubuwan da zai tattatuna da Mai girma shugaban Najeriya idan sun zauna.
Matsalar takaran APC a kasa
Abin da hukumar tsaron ta fahimta shi ne tikitin Musulmi da Musulmi zai kawo rudani a Najeriya, ya kuma kara jawo a rika kai wa Kiristocin kasar nan hare-hare.
Musulmi da Musulmi: Kada ku yarda wani fasto ko limami ya fada maku wanda za ku zaba, Keyamo ga yan Najeriya
Jaridar ta rahoto majiyar yana cewa idan Musulmai suka dare kujerar shugaban kasa da na mataimaki a 2023, jami’an tsaro za su yi fama da kalubale sosai.
Ba gaskiya ba ne - Garba Shehu
Kawo yanzu jaridar da ta kawo wannan labari ba ta iya fitar da wasikar da ta ce an aika fadar shugaban kasar ba, Amma an ji gwamnati ta musanya labarin.
Malam Garba Shehu mai magana da yawun bakin shugaban kasa ya fitar da jawabi, ya na karyata rahoton, ya ce wasu ne ke neman kawo rashin jituwa a APC.
Shettima ba zai koma Majalisa ba
A daidai wannan lokaci ne kuma aka ji labari jam’iyyar APC ta dakatar da gabatar da Kashim Shettima a matsayin 'dan takaran mataimakin shugaban Najeriya.
Ana haka aka ji labari Jam'iyyar APC mai mulki ta zabi Kaka Shehu Lawan a matsayin dan takaran da zai maye gurbin Kashim Shettima a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng