Da Duminsa: Babu sunan Kwankwaso da Sawore a shafin INEC saura ƙiris lokaci ya cika
- Saura kwana uku wa'adi ya kare, hukumar INEC ta ce jam'iyyun NNPP da AAC ba su shigar da sunayen yan takararsu a matakin jihohi ba
- Festus Okoye, kwamishinan INEC mai kula da sashin tattara bayanai, ya ce ba gudu ba ja da baya, ranar 15 ga watan Yuli INEC zata rufe
- Hukumar INEC na amfani da wannan damar somin tuna wa dukkan jam'iyyu cewa awanni 72 ya rage, inji Okoye
Abuja - Yayin da ya rage saura kwana uku kacal a rufe karɓam sunayen yan takara a zaɓen 2023, har yanzu jam'iyyar NNPP da African Action Congress AAC ba su shigar da sunayen yan takarar gwamna da yan majalisun tarayya a shafin INEC ba.
Vanguard ya rahoto cewa yayin da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, ke takarar shugaban ƙasa a NNPP, mai jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, ne ɗan takarar kujera lamba ɗaya karkashin AAC.
Dukkan jam'iyyun biyu ba su miƙa sunayen yan takarar su a matakin jihohi ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ba har zuwa yanzu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Da yake ƙarin haske kan matakan tsaida yan takara, kwamishinan INEC mai kula da sashin yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa kuri'a, Festus Okoye, ya ce sun karɓi Fom 6,995da jam'iyyu 16 cikin 18 suka shigar na matakai daban-daban.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Sai dai jam'iyyu biyu, AAC da NNPP, har yanzu ba su tura mana ko Fom ɗaya ba hanyar shafin yanar gizo-gizo da aka tanada," inji shi.
Kamar yadda jadawalin da INEC ta fitar ya bayyana, dukkan jam'iyyun siyasan da suka kammala halastaccen zaɓen fidda gwani na takarar gwamna, mataimaki da yan majalisun jihohi, an umarci su cike Fom a shafin da INEC ta ware (ICNP) daga 1 zuwa 15 ga watan Yuli.
'Yan ta'adda sun nemi a tattara musu Biliyoyin Naira na fansar Fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna da suka rage
Okoye ya ƙara da cewa:
"Hukumar zaɓe na ƙara tunatar da dukkanin jam'iyyu cewa suna da ragowar kwanaki uku ne su shigar da sunayen yan takarar su a ICNP. Ranar rufe wa tana nan 15 ga watan Yuli, 2022, da karfe 6:00 na yamma shafin zai rufe kansa."
A wani labarin kuma Rikicin APC ya kara ƙamari bayan zaɓo mataimakin Tinubu, wani babban ƙusa ya fice daga jam'iyyar
Batun zaɓo Musulmi a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na APC ya bar baya da ƙura a cikin jam'iyyar.
Tsohon shugaban hukumar soji ta ƙasa kuma babban ƙusa a APC, AVM Frank Ajobena, ya sanar da fita daga jam'iyya mai mulki.
Asali: Legit.ng