Babu yankin da zai iya samar da shugaban kasa shi kadai, inji kungiyar Afenifere

Babu yankin da zai iya samar da shugaban kasa shi kadai, inji kungiyar Afenifere

  • Kungiyar Afenifere ta bukaci yankin kudu Maso Yamma ta hada kai da sauran yankunan kasar dan ganin Tinubu yayi nasara a zaben mai zuwa
  • Afenifere ta yi kira da jiga-jigan yan siyasan yankin kudu maso Yamma da su cire son rai da kiyayya dake tsakanin su dan ganin mulki ya dawo yankin
  • Michael Ogungbemi ya yaba shugaba Buhari da yayan jam'iyyar APC da suka tabbatar da nasarar Tinubu a zaben fidda gwani

Jihar Ekiti : Kungiyar Afenifere ta bukaci ‘yan siyasa daga yankin Kudu maso Yamma da su hada kai da sauran shiyyoyi biyar na kasar domin tabbatar da aniyar tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu, na zama shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa ya yiwu. rahoton PUNCH

Kara karanta wannan

Kafin 2023: Tashin hankali a APCn Katsina, dubban mambobi sun fece zuwa PDP

Sakataren Yada Labarai na Afenifere, Michael Ogungbemi, ya yabawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kungiyar gwamnonin APC, yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC da suka janye wa Tinubu da ‘ya’yan jam’iyyar da suka yi ruwa da tsaki dan ganin ya samu damar tsayawa takarar, inda suka ce:

“Yanzu lokaci ya yi da yankin Kudu maso Yamma za su nuna hadin kan da ba a taba gani ba don nuna wa ‘ya’yan jam’iyyar APC godewa.

Ogungbemi, wanda ya yi magana a wani taron manema labarai a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce,

“Wannan ba lokaci ba ne da za a sanya toga na son rai da kiyayyar da aka yi a baya. Dole ne mu tsara wani sabon tsari kuma mu yi aiki tuƙuru da sauran shiyyoyi biyar na ƙasar don Asiwaju Tinubu ya hau kan karagar mulki .

Kara karanta wannan

Shugaban Ohanaeze yayi tsokaci akan rashin nasarar Ibo a zaben fidda da gwanin da ya gabata

asiwju
Babu yankin da zai iya samar da shugaban kasa shi kadai, inji kungiyar Afenifere
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Tarihin zabe a Najeriya tun daga 1999 ya nuna cewa babu wani yanki na siyasa da zai iya samar da shugaban kasa shi kadai ba tare da hazaka da hadin kan wasu ba.
“Sabo da haka,ya zama dole ne mu yi watsi da son zuciya da kalamai masu kawo rarrabuwar kawuna tare da kafa gaggarumar hadin gwiwa da kabilun Igbo, Fulani, Hausawa, Kanuri da sauran kabilun kasar domin nuna goyon baya ga Asiwaju Tinubu a zabe mai zuwa.
“Muna, kira cikin girmmawa da ladabi ga mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Cif Bisi Akande, Shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Yamma, Rotimi Akeredolu;,Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Dr Kayode Fayemi, Ibikunke Amosun, Rauf Aregbesola da sauran jiga-jigan masu fada a ji da suyi sassanci a tsakanin su dan tabbatar da Asiwaju yayi nasara", inji shi.

Kara karanta wannan

Tinubu, zai bayyana Shettima ko Zullum a matsayin mataimakinsa

Peter Obi baya kyamar mutanen arewa, karya ake masa: Inji hadimin sa

A wani labari, A wani labarin : Mai Magana da yawun bakin dan tankarar shugabankasa a jam’iyyar Labour party LP, Mista Peter Obi, ya musanta rahoton dake nuna maigidansa mai tsaurin ra'ayin addini ne kuma yana kyamar mutanen arewa.

Valentin Obienyem, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce wasu kungiyoyi da ba’a san su ba, wadanda ‘yan adawar siyasa ke daukar nauyinsu, ke yada karya kan Obi saboda karuwar farin jininsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Tofa avatar

Ibrahim Tofa