Barakar PDP ta ki dinkewa, Wike ya yi watsi da wanda Atiku ya tura kasar waje ayi sulhu
- Atiku Abubakar ya tura Adamu Maina Waziri domin ya yi magana da Nyesom Wike a kasar Turkiyya
- Adamu Waziri ya je har otel din da Gwamnan Ribas yake domin su hadu, amma hakan ba ta yiwu ba
- ‘Dan takaran na PDP yana so ya sasanta da Wike ne bayan ya ki daukarsa a matsayin abokin takara
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Turkey - A ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni 2022, Nyesom Wike ya ki bada dama ya zauna da tsohon Ministan harkokin ‘yan sanda, Adamu Maina Waziri.
Jaridar Premium Times ta samu labari cewa Atiku Abubakar ne ya aika Adamu Waziri ya yi magana da Nyesom Wike domin a iya shawo kan Gwamnan.
A halin yanzu akwai sabani tsakanin Gwamnan na jihar Ribas da Atiku Abubakar wanda PDP ta tsaida a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023.
Wike wanda yana kasar Turkiyya, ya ki ba Adamu Waziri damar da za su zauna domin su tattauna, har a iya maganin rikicin da yake neman barkewa.
Kamar yadda jaridar ta fitar a wannan rahoto na musamman, ta ce Atiku ya aika tsohon Ministan ne bayan ya yi ta kokarin haduwa da Wike, abin ya faskara.
Haduwar Atiku da Wike ta gagara
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya nemi ya zauna da Gwamnan jihar Ribas tun kwanaki, domin yi masa bayanin cewa ba zai zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar bai iya ganawa da Wike ba a lokacin domin ya koma Ribas bayan fahimtar cewa Atiku ya natsu da Dr. Ifeanyi Okowa.
Haka zalika an samu labari cewa Gwamnan ya ki bari ya yi magana Atiku Abubakar a waya salula, bai kuma ba wadanda aka aiko su zauna hadin-kai ba.
Adamu Maina Waziri ya je Istanbul
Da jin labarin Wike ya na kasar Turan, na-kusa da Atiku Abubakar sun bayyana cewa sai ya aika tsohon Ministan, wanda ya bi shi har zuwa otel dinsa a Istanbul.
Rahoton ya tabbatar da cewa Wike ya yi kicibis da Alhaji Adamu Waziri a Hilton Conrad Hotel, duk da ya haka, ya ki bari a isar masa da sakon Wazirin Adamawa.
Tsohon Ministan tarayyan ya tuntubi manyan PDP a Najeriya ta wayar salula domin su lallabi Mai girma Wike ya yi magana da shi, amma sam abin ya ci tura.
Daga baya dai an ga hoton Gwamna Wike yana sararawa a kasar ketaren, ya yin da ake jita-jitar cewa zai hadu da 'dan takaran shugaban kasa na APC, Bola Tinubu.
Ba za mu bi Atiku ba - Fayose
A baya an ji labari Ayo Fayose yana cewa da bakinsa Atiku Abubakar ya yi wa Nyesom Wike alkawarin zai zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a PDP.
Ayo Fayose ya ce Wike ba zai taba bin Atiku Abubakar ba tun da ya ci amanarsa, kuma su na tare da Wike 100%, amma idan ya ce a bi Atiku, to dole su yi watsi da shi.
Asali: Legit.ng