An rantsar da Gwamna Ganduje matsayin shugaban kwamitin kamfen gwamnan Osun
- Jam'iyyar APC ta rantsar da kwamitin mutum 81 da zasu taya ta yakin neman zaben gwamnan jihar Osun a watan Yuli
- Gwamnan jihar Kano aka baiwa hakkin tabbatar da APC ta lashe zaben jihar Osun da zai gudana watan gobe
- Gwamna Gboyega Oyetola na neman zarcewa kan kujerar mulki bayan shekaru hudu na farko
Abuja - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta rantsar da kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Osun da zai gudana a watan Yuli, 2022.
Shugaban uwar jam'iyyar, Sanata Abdullahi Adamu, a ranar Alhamis ya rantsar da kwamitin ne a sakatariyar jam'iyyar dake birnin tarayya Abuja.
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ne shugaban kwamitin tare da Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.
Kalli hotunan:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta zabi Ganduje ya jagoranci yakin neman zaben Gwamnan jihar Osun
Uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ta sanar da mambobin kwamiti mutum 81 da zasu yiwa jam'iyyar yakin neman zaben gwamnan jihar Osun.
Hukumar INEC zata gudanar da zaben gwamnan jihar ne ranar 16 ga Yuli, 2022.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan Legas Babajide Sanwoolu, aka nada su jagoranci kwamitin.
A jerin sunayen da shugaban uwar jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu, ya fitar ranar Talata, yace an baiwa wannan kwamiti hakkin tabbatar da cewa dan takarar jam'iyyar, Gboyega Oyetola, ya lashe zaben.
Asali: Legit.ng