APC ta kawo karshen rigimar cikin gidan da aka yi shekaru 8 a jere ana gwabzawa
- A karshe dai rigimar cikin gidan da jam’iyyar APC ta ke fama da shi a jihar Abia zai zama tarihi
- Jagororin jam’iyyar na reshen Abia da suke fada da junansu, sun ajiye makamansu a halin yanzu
- Donatus Nwankpa ya yarda zai yi aiki tare da bangaren Cif Ikechi Emenike domin a kai ga ci a 2023
Abia - Bangarorin da ke rigimar shugabanci a jihar Abia za su dawo karkashin rumfa daya. Jaridar PM News ta ce an yi nasarar kawo karshen rigimar.
A halin yanzu an tabbatar da cewa babu wanda ya yi nasara, kuma babu wanda ya sha kasa a rigimar Donatus Nwankpa da Ikechi Emenike a jihar Abia.
Tun a 2014 aka samu sabani tsakanin Cif Donatus Nwankpa da Cif Ikechi Emenike a reshen jihar.
A dalilin haka mutanen Nwankpa suka tsaida Anyim Nyerere a matsayin ‘dan takarar gwamna. Bangaren Emenike suka fitar da Dr. Emmanuel Ndukwe.
Daga 2014 har zuwa zaben 2019
Wannan rikici ya kai har zuwa zaben 2019, yayin da Uche Ogahya ya samu tikiti, a gefe guda yana fuskantar barazanar ‘yan tawarensu Cif Ikechi Emenike.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A karshe wadannan bangarori biyu sun yi zama a gidan tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayya, Hon. Emeka Atuma a ranar Asabar dinnan da ta gabata.
PM News ta ce an tashi wannan zama da alkawarin za a hada-kai domin a cin ma nasara tare a 2023.
Da suke yi wa magoya bayansu bayani bayan taron, Donatus Nwankpa da Ikechi Emenike sun tabbatar da cewa dogon yakin da ake yi ya zo karshe.
Abokan gaban junan sun bayyana cewa a siyasa babu gabar din-din-din, don haka sun sasanta. A cewarsu, silar rikicinsu shi ne a kawowa jihar cigaba.
“Wannan sabuwar APC ce. Mun tattauna da juna, kuma za a ba kowa ayi da shi. Mun zo da sabon shiri, burinmu shi ne mu karbe Abia a zaben 2023.”
- Donatus Nwankpa
Vanguard ta ce shi ma Emenike ya yi jawabin murna, ya na mai kira ga mutanensu da su yi azumin kwanaki uku domin Ubangiji ya kawo masu sauyi.
Ku na da labari Muhammadu Buhari zai bar Najeriya, zai halarci taron CHOGM tare da mukarrabansa. Daga ciki akwai Isa Ali Pantami da wasunsa.
Femi Adesina yace abokan rakiyar su ne: Geoffrey Onyeama; Zainab Ahmed; Osagie Ehanire; da Mohammed Abdullahi.
Asali: Legit.ng