Da duminsa: Kwankwaso ya zabi Barista Ladipo Johnson matsayin mataimakinsa

Da duminsa: Kwankwaso ya zabi Barista Ladipo Johnson matsayin mataimakinsa

Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta alanta cewa ta zabi Barista Ladipo Johnson a matsayin abokin tafiyar dan takarar shugaban kasar jam'iyyar, Rabiu Musa Kwankwaso.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Johnson wanda dan asalin jihar Legas ya yi takarar gwamna jihar.

NNPP tayi wannan sanarwa ne a shafinta na Tuwita, @nnpphqabuja1, kuma Kakakin jam'iyyar, Major Agbor, ya tabbatar da hakan, rahoton Leadership.

Jawabin yace:

"Barr Ladipo Johnson ne dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasar jam'iyyarmu mai girma."
Kwankwaso
Da duminsa: Kwankwaso ya zabi Barista Ladipo Johnson matsayin mataimakinsa Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel