Bidiyo: Dan Majalisar Tarayyar Najeriya Ya Bada Umurni An Nuna Alat Din Albashinsa Na Watan Mayu a Talabijin

Bidiyo: Dan Majalisar Tarayyar Najeriya Ya Bada Umurni An Nuna Alat Din Albashinsa Na Watan Mayu a Talabijin

  • Dan majalisar wakilai na tarayyar Najeriya ya nuna wa duniya adadin kudin da ya ke samu matsayin albashin watan Mayu
  • Honarabul Leke Abejide, mai wakiltar Yagba East/West/Mopamuro a majalisa ta tara ya ce N697,000 ne albashinsa duk wata
  • Abejide ya kara da cewa allawus dinsa kuma yana amfani da su wurin biyan yan sanda masu tsaronsa, ma'aikatansa, hadimai da mutanen mazabarsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Honarabul Leke Abejide, dan majalisar tarayya mai wakiltar Yagba East/West/Mopamuro a majalisa ta tara ya ce N697,000 ne albashinsa duk wata.

Dan majalisan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily a gidan talabijin na Channels TV inda ya bada umurni a nuna alert dinsa na banki.

Dan Majalisa Hon Leke Abejide.
Bidiyo: Dan Majalisar Tarayyar Najeriya Ya Bada Umurni An Nuna Alat Din Albashinsa Na Watan Mayu a Talabijin. Hoto: @ChannelsTV.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kamfanonin Jiragen Sama a Najeriya Za Su Tsayar Da Aiki Saboda Tsadar Man Jirgin Sama

Da aka tambaye shi game da batun allawus bayan albashi, dan majalisar ya ce:

"Batun allawus da ku ke magana, na fada muku a matsayin sabon mamba, domin in gamsar da yan mazabata na yi amfani da allawus dina baki daya; na farko, ina da yan sanda, ina da hadimai, mutanen mazabata suma suna jira na, don haka a wata bana tunanin ina samun abin da ya kai N1.5m.
"Kuma ina da iyali da na ke kula da su, akwai lokacin da na ke tunanin zan tsere, idan kai dan kasuwa ne kuma ka shigo majalisa, ba za ka so ka cigaba ba domin abin da mazabarka ke nema daga wurin ka duk wata ya kai miliyan 30 zuwa 40".

Ya cigaba da cewa saboda kusancin dan majalisa da mutanensa, dukkan bukatunsu wurinsa suke zuwa domin ba za su iya ganin gwamna ba kuma idan baka musu ba, za su ce baka komai.

Kara karanta wannan

Kiyayya Ta Makantar Da Kai: Femi Adesina Ya Caccaki Oyedepo Kan Alkanta Gwamnatin Buhari Da Rashawa

Abejide ya ce idan mutum ba mai hali bane tun kafin ya zo majalisa, akwai yiwuwar mutanensa za su fara jifansa da dutse cikin shekara guda.

Ekiti 2022: 'Idan Ba Kuri'a, Ba Kudi', Bidiyon Tinubu Yana Yi Wa Masu Zabe Ba'a a Wurin Kamfen

A wani rahoton daban, Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci al'ummar Jihar Ekiti su fito su yi zabe idan ba hakan ba ba za a biya su ba.

Tinubu, wanda ya ziyarci a Jihar Ekiti a ranar Talata ya furta hakan ne wurin yakin neman zabe na dan takarar gwamna na jam'iyyar, Biodun Oyebanji gabanin zaben da ake shirin yi ranar Asabar 18 ga watan Yunin 2022.

Ya kuma kambama kansa cewa bai taba fadi zabe ba a baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164