Daga karshe, Atiku Abubakar ya zaɓi wanda yake so ya zama mataimakinsa a 2023
- Bayan dogon lokaci ana kace nace, wasu bayanai sun tabbatar da cewa Atiku Abubakar ya zaɓi wanda ya ke so ya zama abokin takararsa
- Jam'iyyar PDP ta tsinci kanta cikin ƙaƙanikayi game da wanda zai zama mataimaki, sai dai Gwamna Wike da Okowa ne a sahun gaba
- Yayin da kwamitin da PDP ta kafa domin lamarin ya zaɓi gwamna Wike, majiya kusa da Atiku tace ɗan takaran ya fi son gwamna Okowa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, zai gabatar da ɗan takarar mataimaki da ya zaɓa a tsakar ranar nan, Alhamis 16 ga watan Yuni, 2022.
Makusantan tawagar yaƙin neman zaɓen Atiku sun bayyana cewa za'a sanar da zaɓin da ƙarfe 12:00 na rana kuma bayan haka Kwamitin da aka kafa zai tantance shi.
Hakan ya biyo bayan jerin taruka da ɗan takarar ya gudanar da manyan ƙusoshin jam'iyya jiya Laraba da daddare.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa har zuwa yau Alhamis da safe gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, shi ne zaɓin Atiku Abubakar na ƙarshe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani na kusa da kungiyar Kanfe ɗin Atiku ya ce:
"Indai ba canjin zaɓi aka samu a mintin ƙarshe ba, Gwamna Okowa ne za'a sanar da safiyar nan amma kunsan cewa a siyasa minti ɗaya ma yana da tsayi."
Kakakin ɗan takarar na PDP, Paul Ibe, ya ƙi tsokaci kan sunan ɗan takarar mataimaki da aka zaɓa, inda ya faɗa wa jaridar cewa su jira a sanar a hukumance.
Ive ya ce:
"Abinda zan iya cewa shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa ya damu ya kammala batun zaɓo abokin takara saboda ya maida hankali kan mataki na gaba na kwace mulki daga hannun APC."
"Wanda ɗan takarar zai zaɓa ba bu tantama kowane ɗan Najeriya mai ƙishi zai ji daɗinsa a cikin zuciya."
Shin Okowa PDP ta zaɓa?
A nata ɓangaren jam'iyyar PDP ta kafa kwamitin da zai bai wa Atiku shawari kan yan takarar da ya dace ya zaɓa a matsayin abokin takara.
Amma duk da rahoton da ya hito cewa kwamitin ya ba da shawari kan gwamnan Ribas, Nyesom Wike, zaɓin kwamitin bai kwanta wa da yawan shugabannin PDP ba.
A wani labarin kuma bayan Sauya sheka zuwa APC, Majalisar dokokin jihar Oyo ta fara shirin tsige mataimakin gwamna
Bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, majalisar dokokin Oyo ta fara shirin tsige mataimakin gwamna, Rauf Olaniyan.
Bayan kara n ta ƙorafi kan mataimakin gwamnan, yan majalisa 24 cikin 32 suka sa hannun don cigaba da bin matakan tsige shi.
Asali: Legit.ng