Yanzu-Yanzu: Zamu bayyana sunan mataimakin Atiku Abubakar nan da awanni, PDP
- Jam'iyyar PDP ta bukaci yan Najeriya su ƙara hakuri domin nan da yan awanni kaɗan zata fito ta bayyana mataimakin Atiku a zaɓen 2023
- Mai magana da yawun PDP ta ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce shugabannin PDP na ta kokarin zaɓo wanda kowa zai marhabun da shi
- Ya ce kwamitin ayyuka ya gudanar taro yau kan lamarin amna ba shi da adadin mutanen da za'a tantance gobe
Abuja - Babban jam'iyyar hamayya ta ƙasa PDP ta sanar da cewa zata bayyana ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2023 nan da yan awanni kalilan.
Kakakin jam'iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa ya kamata yan Najeriya su ƙara hakuri yayin da PDP ke cigaba da bin matakan demokaradiyya don zakulo wanda kowa zai marhabun da shi.
2023: PDP na tsaka da kokarin zaɓo mataimakin Atiku, Sanata mai ci ya sauya sheƙa zuwa APC a hukumance
Kakakin PDP ya ƙi ya bayyana sunayen yan takarar mataimaki da jam'iyya ta haɗa, waɗan da kwamitin Chief Tom Ikimi zai tantance.
Ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Bani da adadin mutanen da za'a tantance gobe, bansan yawan su ba. Kwamitin ayyuka NWC ya gudanar da taro yau kuma yana cikin matakan shawari da ake cigaba da yi a cikin jam'iyya."
"Ya kamata mu jira yi sakamakon waɗan nan matakai, muna da lokaci daga nan zuwa Jumu'a amma nan da yan awanni za'a kammala komai."
Mun ba kowa haƙkinsa a jam'iyya - PDP
Mista Ologunagba ya ƙara da cewa saɓanin rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta, Kwamitin da Umaru Damagum ke jagoranta an haɗa shi wuri ɗaya.
"Ɗan takara ya bukaci a jawo kowa a jiki kan lamarin, wanda ya haɗa da masu ruwa da tsaki da sauran sassan jam'iyya. Mun faɗaɗa shawari ta yadda kowane mamba zai ji a ransa ana yi da shi."
"Haka muka saba yi a matsayin jam'iyya, duk abubuwan da muka yi zasu fito kuma ya ƙare da bayyana ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa. Ina da yaƙinin cewa nan da yan awanni za'a bayyana shi."
A wani labarin kuma Bayan sauya sheka zuwa APC, Kujerar mataimakin gwamnan PDP ta fara tangal-tangal, Majalisa zata tsige shi
Bayan ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, majalisar dokokin Oyo ta fara shirin tsige mataimakin gwamna, Rauf Olaniyan.
Bayan kara n ta ƙorafi kan mataimakin gwamnan, yan majalisa 24 cikin 32 suka sa hannun don cigaba da bin matakan tsige shi.
Asali: Legit.ng