Hadimin Buhari Ya Bada Satar Amsa Kan Wanda Zai Zama Abokin Takarar Tinubu
- Ga tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, cancanta ne babban abun dubawa wajen zabar wa Bola Tinubu abokin tafiya
- Tsohon hadimin shugaban kasar ya wallafa wannan ra'ayin ne a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 13 ga watan Yuni
- Ahmad ya yi nuni da hakan ne duk da har yanzu 'dan takarar shugaban kasar jam'iyyar APC bai zabi wanda yake so su yi tafiyar tare ba, 'yan Najeriya suna da tabbacin ba zai yi zaben banza ba
Bashir Ahmad, tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi magana a kan abun da 'yan Najeriya ya kamata su maida hankali a kai yayin da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ke cigaba da neman abokin tafiya.
A wata wallafar da ya yi a Twitter ranar Litinin, 13 ga watan Mayu, Ahmad ya ce cancanta shi ne babban abun dubawa yayin neman wanda zai zama abokin tafiyar Tinubu a jam'iyyar APC.
Mataimakin shugaban kasa: Daga karshe Tinubu ya fayyace gaskiyar lamari kan tikitin Musulmi da Musulmi
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tsohon hadimin ya ce duk da ba a san wanda Tinubu zai dauka a matsayin mataimaki ba, 'yan Najeriya sun tabbata wanda ya san makamar aiki za a zaba.
"Ga yawancin mu, wadanda a shirye muke da mu zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar mu shekara mai zuwa, mun damu matuka da cancantar mataimakin da zai zaba kwanan nan, sai yarensa ko addininsa.
"Ba mu da masaniya game da addinin mataimakin da za a zaba, amma muna da tabbacin ya cancanta."
Kwamitin ayyuka na APC (NWC) sun bayyana yadda suke zargin cewa Tinubu zai zabi tsohon gwamnan arewa a matsayin abokin tafiyarsa.
Saidai, mambobin kwamitin ayyuka na APC (NWC) sun bayyana yadda masu rike da mukaman arewa suka zabi Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin tafiyar Ahmed Tinubu, 'dan takarar shugaban kasar jam'iyya mai mulki.
Wani mambar NWC wanda ba za a iya ambatar sunansa ba, ya bayyana yadda ake zargin masu rike da mukaman arewa suke ganin Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno a zabin da yafi tsohon kakakin majalisar dattawa, Yakubu Dogara da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wadanda ake tunanin tsaidawa.
Mamban NWC, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce "bayan dubi tare da nazari, mun amince da Sanata Shettima. Zai ba mu kuri'un da muke bukata."
Asali: Legit.ng