Da Dumi-Dumi: Atiku Abubakar ya taya Bola Tinubu murnar lashe tikitim APC

Da Dumi-Dumi: Atiku Abubakar ya taya Bola Tinubu murnar lashe tikitim APC

  • Ɗan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya aike da sakon taya murna ga jagoran APC na ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Atiku ya tura sako ne biyo bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na fitar da ɗan takara a Abuja
  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya jinjina wa Tinubu, inda ya ce jajircewarsa ce kaɗai ta yi saura daga ƙarshe

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa da jam'iyyar PDP ta tsayar, Alhaji Atiku Abubakar, ya taya jagoran APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, murnar samun nasara.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan ya ta ya Tinubu murnan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na dandanlin sada zumunta Tuwita.

Kara karanta wannan

K'ayatattun Hotunan Shugaba Buhari yayin miƙa tuta ga ɗan takarar shugaban ƙasa a APC

Bola Tinubu tare da Atiku.
Da Dumi-Dumi: Atiku Abubakar ya taya Bola Tinubu murnar lashe tikitim APC Hoto: Ivory NG
Asali: UGC

Tinubu, ya lashe zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC bayan shafe kwanaki ana gudanar da babban taron APC na musamman a Abuja.

Da yake taya jagoran APC na ƙasa murna, Atiku ya ce bayan dogon lokaci ana fafatawa daga ƙarshe jajircewar ɗan takaran ce ta rinjaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku Abubakar ya ce:

"Ina taya murna ga Bola Tinubu @OfficialABAT bisa zama ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyarka. Bayan shafe lokacin ana fafata wa, amma daga ƙarshe jajircewarka ce ta rinjaya."

Yadda za'a fafata a 2023

Bayan samun wannan nasara, Tinubu na jam'iyyar APC zai fafata da Atiku Abubakar na PDP da sauran yan takara na sauran jam'iyyu masu rijista a babban zaben 2023 da ke tafe.

Sai dai ana ganin faɗan zai fi zafi tsakanin manyan jam'iyyu biyu, APC da PDP, sai kuma jam'iyyar NNPP mai kayan marmari da wasu ke ganin zata ba da mamaki a 2023.

Kara karanta wannan

Zaben fidda dan takarar shugaban kasa na APC: Jerin yan takara 4 da basu samu kuri’a ko daya ba

A yau Laraba 8 ga watan Yuni, 2022, jam'iyyar NNPP ke gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa. Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, shi ne kaɗai ɗan takara.

A wani labarin kuma 'Yan takarar shugaban kasa 7 da suka janye wa Bola Tinubu a filin babban taron APC

Bayan tsayin dare ana kaɗa kuri'u da duk abinda ya biyo baya, kwamitin zaɓe ya sanar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe tikitin shugaban kasa.

Wasu yan takara sun sadaukar wa Tinubu da burin su, inda suka janye kuma suka mara masa baya, mun tattaro muku su duka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262