Yanzu-yanzu: Asiwaju Bola Tinubu ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar APC
- Bayan kwanaki biyu da deleget suka taru a farfajiyar Eagle square Abuja, an sanar da sakamako
- Asiwaju Bola Tinubu ya samu gagarumar nasara kan tsohon minista Chibuike Rotimi Amaechi
- Sauran yan takaran da suka dan tabuka kokarin sune mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da Ahmad Lawan
Abuja - Tsohon gwamna jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya lashe zaben fidda gwanin yan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC.
A zabensa na farko tun bayan barin mulki a 2007, Tinubu yanzu shine zai wakilci jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa a zaben shekarar 2023.
Tinubu ya lallasa yan takara 12 da suka fafata a zaben inda ya samu kuri'u sama da 1,271
Wanda ya zo na biyu shine tsohon Gwamnan jihar Rivers, kuma tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi wanda ya samu kuri'u 316.
Sannan Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya samu kuri'u 235.
Shugaban kwamitin zaben kuma Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya alanta Tinubu matsayin zakara a zabe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu yanzu zai fafata da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP dss a ranar 25 ga Febrairu, 2023.
Ga jadawalin sakamakon:
S/N | Sunayen yan takara | Adadin Kuri'in da suka samu |
1 | Asiwaju Bola Tinubu | 1,271 |
2 | Rotimi Amaechi | 316 |
3 | Farfesa Yemi Osinbajo | 235 |
4 | Ahmad Lawan | 152 |
5 | Yahaya Bello | 47 |
6 | Sani Ahmed Yarima | 4 |
7 | Ben Ayade | 37 |
8 | Rochas Okorocha | 0 |
9 | Tunde Bakare | 0 |
10 | Tein Jack Rich | 0 |
11 | Ogbonnaya Onu | 1 |
12 | Dave Umahi | 38 |
13 | Emeka Nwajuiba | 1 |
Asali: Legit.ng