Shugaban APC bai hakura ba, zai gabatar da ɗan takarar da yake so ga Buhari, Kalu
- Sanata Kalu ya bayyana cewa shugaban jam'iyya da sauran yan kwamitin NWC zasu gabatar wa Buhari da ɗan takarar maslaha
- Kalu ya taya shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan murna, bisa nasarar zama ɗan takarar maslaha na APC
- Tun bayan fitar sunan Lawan, Buhari da wasu mambobin NWC sun nesanta kan su da lamarin
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a APC, Sanata Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa shugaban jam'iyya, Abdullahi Adamu, da kwamitin gudanarwa NWC zasu gabatar da Lawan ga Buhari.
Punch ta ruwaito cewa Adamu da sauran yan kwamitinsa na NWC zasu kai wa Buhari sunan Ahmad Lawan ne domin ya goya masa baya a matsayin ɗan takarar maslaha.
Rahoton da ya karaɗe kafafen watsa labarai ya nuna cewa Adamu ya zaɓi shugaban majalisar dattawa a matsayin ɗan takarar sulhu yayin da zaɓen fidda gwani zai gudana yau Talata.
Bayan haka ne, Mambobin NWC da kuma shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, suka fito suka shaida wa duniya cewa ba su da hannu a zaɓen ɗan takarar maslaha.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sun jaddada cewa dukkan yan takara zasu haɗu a akwatin zaɓe yayin da Deleget zasu raba gardama kan wanda zai karbi tutar jam'iyya a babban zaɓen dake tafe.
Kalu ya taya Sanata Ahmad Lawan Murna
A wata sanarwa da ya rattaɓa wa hannu. da kansa, Sanata Kalu ya taya Ahmad Lawan murna tare da cewa za'a kai wa Buhari sunansa domin mara masa baya.
Ya ce:
"Bayan dogon nazari kan yan takarar mu da suka cancanta, Sanata Abdullahi Adamu, ya yanke cewa Ahmad Lawan ne ya fi dacewa ya zama ɗan takarar APC a zaben shugaban ƙasa 2023."
'"Shugaban jam'iyya da kwamitin gudanarwa NWC zasu gabatar da sunan Lawan ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, domin ya mara masa baya."
A wani labarin kuma Zaɓen Magajin Buhari: Yan jaridu sun yi cirko-cirko a kofar shiga Filin taron APC kan abu ɗaya
A rana ta biyu na babban taron APC na zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa, ayyuka sun kankama kuma shirye-shirye sun yi nisa.
Sai dai har yanzun yan jaridun da duka je ɗakko abun da ke wakana ba su samu damar shiga ba sanadiyyar gazawar APC.
Asali: Legit.ng