Kai Tsaye: Shugaban INEC Yana Amsa Tambayoyi Kan Zabukan 2023
A yau Asabar, 4 ga watan Yuni ne 'yan Najeriya za su tattauna kan batutuwan zabukan Najeriya na shekara mai zuwa tare da sanin yanayin shirin hukumar zabe mai zaman kanta, INEC.
Taron wanda za a fara da kafe 12 na rana, za a yi shi a cibiyar Shehu Musa Yar'adua da ke Abuja, zai bai wa 'yan Najeriya damar mika tambayoyinsu ga shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, Mahmood Yakubu, kan shirye-shiryen hukumar kan zabukan.
Taron mai taken "Masu zabe", zai samu jagorancin Ebuka Obi-Uchendu, mai gabatarwa na gidan talabijin.
Ku bibiyi Legit.ng inda za ta kawo muku abinda ke faruwa tare da amsar tambayoyin masu zabe kai tsaye.
Dalilinmu na dakatar da rijistar katin zabe ta yanar gizo, Farfesa Mahmud Yakubu
INEC za ta buga takardu 500 miliyan na zabukan 2023, Farfesa Yakubu
Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya ce hukumar za ta buga takardu kusan 500 miliyan domin zabukan 2023.
Za a iya yin zabe ne idan 'yan kasa sun shiga lamarin dumu-dumu, Shugaban INEC
Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Yakubu ya ce za a samu nasarar gudanar da zabukan 2023 idan 'yan kasa sun shiga lamain kai da fata.
Shugaban Hukumar INEC, tare da wasu mambobin hukumar sun iso wurin taron
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu tare da wasu mambobin Hukumar sun isa cibiyar Shehu Musa Yar'adua da ke Abuja.