EFCC ta saki Rochas Okorocha, an tantance shi a matsayin ‘Dan takara kafin a rufe kofa

EFCC ta saki Rochas Okorocha, an tantance shi a matsayin ‘Dan takara kafin a rufe kofa

  • Rochas Okorocha ya bayyana a gaban kwamitin da ke tantance masu yin takara a jam’iyyar APC
  • Sanata Rochas Okorocha yana cikin wadanda suka saye fam na neman kujerar shugaban Najeriya
  • Ana daf da za a soma tantance masu takara a 2023 ne jami’an EFCC su ka cafke tsohon Gwamnan

Abuja - A karshe labari ya zo cewa Rochas Okorocha ya samu ‘yanci. Hakan na zuwa ne bayan ya yi kwanaki a tsare a hannun hukumar EFCC ta kasa.

Sanata Rochas Okorocha ya fito ne bayan ya cika sharudan belin da Alkali ya gindaya masa.

Punch ta ce daga fitowarsa, sai ya wuce wurin da jam’iyyar APC ta ke tantance masu neman takarar shugaban kasa, Transcorp Hilton Hotel a Abuja.

Sanata Okorocha ya hallara wurin ne da kimanin karfe 9:35 na dare. A nan ya fuskanci kwamitin da John Oyegun yake jagoranta na tantance masu takara.

Kara karanta wannan

2023: Duk da nukun-nukun da ake yi, akwai yiwuwar APC ta tantance Jonathan a yau

Za a saki Okorocha - Lauya

Kamar yadda labari ya zo daga daya daga cikin lauyoyin ‘dan siyasar, Steve Asimobi, an tabbatar da cewa dama zai zauna gaban kwamitin da zarar ya fito.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sahara Reporters ta rahoto Steve Asimobi yana tabbatar da cewa za a tantance Okorocha mai neman kujerar shugaban kasa a APC bayan samun beli.

Rochas Okorocha
Sanata Rochas Okorocha Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Asimobi ya ce tun da kotu ta bada belin tsohon gwamnan na jihar Imo, EFCC ta na da zabi; tsare shi a kurkuku ko a hannunta har sai an cika sharudan belin.

A karshe hukumar ta EFCC ta fito da Sanatan bayan da ya biya miliyoyin kudin da aka sa na beli.

A maida masa fasfo - Kotu

Alkalin da ya saurari karar ya umarci jami’an EFCC su maidawa Okorocha takardun fasfonsa na fita ketare. Ana zarginsa ne da laifin satar Naira biliyan 2.9.

Kara karanta wannan

Rochas Okorocha, Lawan da sauran yan takarar shugaban ƙasa 9 da Kwamitin APC zai tantance yau

Babu mamaki Sanatan na yammacin jihar Imo shi ne mutum na karshe da kwamitin na APC ya tantance, bayan an zauna da masu takara 11 a ranar farko.

Tun farko Okorocha ya koka da cewa EFCC ta kama shi ne domin hana shi takarar shugaban kasa, ganin zai iya rasa tantance masu neman takarar da aka shirya.

An tantance Tinubu

Ku na da labari a shekaran jiya ne kwamitin tantance masu takarar shugaban kasa ya zauna da Bola Ahmed Tinubu wanda yana cikin 'yan gaba-gaba a takara.

Bola Tinubu ya yi bayanin abin da ya sa yake neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC. A wurin ya yi bayanin irin nasarorin da ya samu da ya yi gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng