Mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023 zai iya zama Gwamnan da ya yi takara da shi

Mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023 zai iya zama Gwamnan da ya yi takara da shi

Atiku Abubakar ya na neman wanda zai dauko a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban Najeriya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ana tunani ‘Dan takarar na PDP zai zakulo abokin takararsa ne daga yankin kudu maso kudancin kasar

Daga cikin zabin akwai Udom Emmanuel wanda ya yi takara da Atiku wajen samun tikitin jam’iyyar PDP

2023 - Atiku Abubakar wanda zai yi wa jam’iyyar PDP takarar shugaban kasa a shekara mai zuwa yana tunanin wanda zai dauko ya zama masa mataimaki.

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto cewa daga cikin wadanda ake magana akwai Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa da Udom Emmanuel na Akwa Ibom.

Wata majiya ta bayyana cewa tuni Atiku Abubakar ya fara tattaunawa da jagororin jam’iyyar PDP a birnin Abuja bayan ya yi nasara a zaben fitar da gwani.

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

A zaben 2019, Legit.ng Hausa za ta iya tuna Peter Obi ne wanda ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa, amma yanzu yana takara a jam’iyyar LP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zabin Obi ya fusata manyan jam’iyyar PDP musamman daga Kudu maso gabas domin Atiku Abubakar ya dauki mataimaki ba tare da ya tuntube su ba.

Peter Obi ya yi gwamna a jihar Anambra ne a karkashin APGA, don haka ake yi masa kallon bare.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar bayan lashe zabe Hoto: @Atiku.org
Asali: Twitter

Saboda gudun a samu irin wannan matsala, shiyasa ‘dan takarar shugaban kasar ya ke aiki da shugaban PDP, Iyorchia Ayu a kan wanda ya dace ya dauka.

Ifeanyi Okowa ko Udom Emmanuel

Zuwa yanzu, Ifeanyi Okowa da Udom Emmanuel ne ake tunanin su na kan gaba a jerin wadanda ake tunanin Atiku zai iya zaba ya taya shi takara a zaben 2023.

Jaridar ta ce ana la’akari da Ifeanyi Okowa duk da shi ya jagoranci gwamnonin kudancin Najeriya a garin Asaba, su ka nuna adawarsu ga takarar Arewa a PDP.

Kara karanta wannan

Ba zan yi amai na lashe ba: Martanin gwamna Wike da ya sha kaye bayan ganawa da Atiku

Tsohon gwamna James Ibori ne yake da wuka da nama har yanzu a PDP, amma ana ganin Sanata Okowa ya taka rawar gani wajen tikitin da Atiku ya samu.

Wani abin la’akari shi ne Okowa zai iya samun karbuwa a wajen mutanen kudu maso gabas saboda mutanen yankinsa a Delta su na magana da harshen Ibo.

Wani Gwamna da ake hari shi ne Udom Emmanuel mai shekara 55. Kafin hawansa mulki, shi ne sakatare a gwamnatin Godswill Akpabio a karkashin PDP.

Ba za a dauko Ibo ba?

Da wahala Ibo ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa wannan karo domin Okezie Ikpeazu da Ifeanyi Ugwuanyi sun marawa Nyesom Wike baya.

Mutanen jihar Ebonyi a yankin kuma sun zabi Anyim Pius Anyim ne a zaben fitar da gwani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng