Yanzun Nan: Jam'iyyar APC ta tantance gwamnan Jigawa ya fafata a zaɓen fidda gwani
- Yayin da jam'iyyar APC ke cigaba da aikin tantance yan takararta na shugaban ƙasa, an tantance gwamna Badaru na Jigawa
- Kwamitin da APC ta kafa domin tantance duk kan yan takararta, wanda ke karkashin Jonh Oyegun na cigaba da aiki gadan-gadan
- Jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu, da tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, sun isa wurin da yammacin nan na ranar Litinin
Abuja - Jam'iyyar APC ta tantance Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya shiga zaɓen fitar da gwanin jam'iyya da aka shirya farawa ranar 6 ga watan Yuni, 2022.
A ranar Litinin, Kwamitin da ke aikin tantance yan takara karkashin jagorancin John Oyegun, ya tantance gwamnan kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.
A cewar mai taimaka wa gwamnan ta fannin Midiya, Kwamitin ya binciki katin zama ɗan jam'iyya na Badaru, kudin da ya mallaka, takardun karatunsa da sauran abubuwan da kundin mulki ya tanada.
Gwamna Badaru na ɗaya daga cikin yan takarar shugaban ƙasa da suka lale kudi miliyan N100m suka sayi Fom ɗin tsayawa takara a jam'iyyar APC.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A makonnin baya, lokacin da tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya kai ziyara jihar Jigawa, Badaru ya ce a shirye yake ya janye wa Amaechi takara.
A cewarsa, da shi da Rotimi Amaechi duk uban su ɗaya, shi ne shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, duk abin da suke yi sai sun nemi shawararsa.
Yan takara na cigaba hallara wurin tantancewa
Channels tv ta rahoto cewa jangoran jam'iyyar APC na ƙasa, Bola Tinubu, da tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, sun dira wurin tantancewa a Abuja.
Sauran yan takara da suka hallara sun haɗa da Sanata Ibikunle Amosun, gwamnan Ebonyi, Dave Umahi, tsohon ƙaramin ministan ilimi, Emeka Nwajiuba, Fasto Tunde Bakare, Nicholas Felix, Uju Ken-Ohanenye, Ajayi Borofice da Ken Nnamani.
A wani labarin kuma Atiku ya gana da Gwamna Wike bayan lallasa shi a zaɓen fidda gwanin PDP
Atiku Abubakar, ɗan takarar da jam'iyyar PDP ta tsayar a zaɓen shugaban kasa ya gana da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a Abuja.
Tsohon mataimakin shugaban ya yi haka ne a wani yunkuri na sulhu da gwamnan, wanda shi ne ya zo na biyu a samun kuri'u.
Asali: Legit.ng