Kai tsaye: Atiku ya yi nasara a zaben fidda gwani, ya lallasa sauran yan takara 12

Kai tsaye: Atiku ya yi nasara a zaben fidda gwani, ya lallasa sauran yan takara 12

Rana bata karya, a yau Asabar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP za ta gudanar da taron gangami kuma zaben fidda gwanin dan takaran shugaban kasa da wakilceta a zaben 2023.

Taron zai gudana ne a farfajiyar Velodrome na filin kwallon tarayya ta MKO Abiola dake Abuja.

Yan takara 14 zasu fafata a wannan zabe mai tarihi.

Atiku, Wike, Tambuwal, Saraki
Atiku, Wike, Tambuwal: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau Hoto: TheNation
Asali: Facebook

Atiku ya yi nasara a zaben fidda gwani, ya lallasa sauran yan takara 12

Alhaji Atiku Abubakar ya samu nasara a zaben fidda gwanin da ke gudana a Abuja.

A bisa sanarwar shugaban kwamitin zabe, Atiku ya lallasa sauran yan takara inda ya samu kuri'u 371

Wanda ke biye da shi shine gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, wanda ya samu kuri'u 237.

An kammala kada kuria, an fara kirga

Deleget guda 767 sun kammala kada kuri'unsu a zaben fiddan gwanin dake gudana a Abuja.

Yanzu an fara kirgen kuri'un.

Atiku ya godewa Tambuwal

Alhaji Atiku Abubakar ya mika godiyarsa ga Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, wanda ya janye masa.

Deleget sun fara kada kuri'a

Deleget fari da na jihar Abia sun fara kada kuri'unsu, sannan na Adamawa,

Tambuwal ya janyewa Atiku a takarar shugaban kasa

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya janyewa Alhaji Atiku Abubakar.

Ya yi kira ga mabiyansa su kadawa Atiu dukkan kuri'un da suka niyyar ka'da masa.

Atiku, Wike, Saraki: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau
Atiku, Wike, Saraki: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau
Asali: UGC

Yan takara sun fara kaddamar da jawabansu

Udom Emmaneul a jawabinsa yace shi mutum ne mai ilimi kuma mai kuzari wanda zai dawo da martabar Najeriya idan ya zama shugaban kasa

Ayo Fayose a nasa jawabin, yace a tarihin siyasarsa, ya kayar da jam'iyyar dake mulki sau biyu lokacin da yayi Gwamna a jihar Ekiti. Saboda haka idan aka zabeshi, zai yi waje da jam'iyyar APC.

Chikwendu Kalu yace yana da ilimi kuma ya san abinda zai yi muddin ya zama Shugaban kasar Najeriya

Gwamna Bala Mohammed Kauran Bauchi a nasa jawabin yace ya fahimci Najeriya sosai kuma jama'a sun shaida lokacin da yake Minista a Abuja, hakazalika yanzu dake gwamna a jihar Bauchi.

Dele Momodu ya kakanninsa Musulmai ne amma Iyayensa Kirista ne. Game da ilimi, daga gidan Malamai ya fito saboda haka zai baiwa Najeriya Ilimi.

Sam Ohabunwa yace shaidanu sun lalata Najeriya, sun mamaye Najeriya da rashin tsaro da rashawa. Ya ce yana da tsari a kaa na yadda za'a kawar da talauci.

Tari Diana Oliver tace a Legas aka haifeta, babanta dan Delta, uwarta ya Imo saboda itace cikakkiyar yar Najeriya.

Bukola Saraki a nasa jawabin yace wajibi ne a zabi dan takaran da ya san abinda yake kuma zai iya hada kan yan Najeriya kuma shine wanda zai iya hakan.

Aminu Waziri Tambuwal a nasa jawabin yace jajircewarshi da kwazonshi da sanin ya kamata yaga ya dace ya mulka kasar, yace ban yi yaro da na mulka Nijeriya ba kuma ban yi tsufa ba

Nyesom Wike yace a yau duk wanda yaci zaben fidda gwanin nan a PDP zan goyi bayanshi dari bisa dari, matsalar Nijeria a yau itace jagoranci, PDP tana bukatar jajirtacce wanda zai iya karawa da APC, saboda haka nine wannan, nine zanyi nasara, nine zanyi nasara, nine zanyi nasara

Shugaban uwar jam'iyyar PDP ya bude taro

Shugaban uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party, Senator lyorchia Ayu, ya bude taron gangami kuma zaben fidda gwanin dan takara shugaban kasa.

Wannan bude taro da yayi ne zai kaddamar da taron.

Atiku, Wike, Saraki: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau
Atiku, Wike, Saraki: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau
Asali: Twitter

Likita kuma dan takara, Nwachukwu Anakwenze, ya janyewa Nyesom Wike

Wani Likita mazauni Amurka da ke neman takara kujeran shugaban kasa karkashin PDP, Dr. Nwachukwu Anakwenze, ya sanar da janyewa daga takarar saboda rashin baiwa yankin Igbo tikiti.

A cewarsa, tun da abin ya zama haka, yanzu yana bayan Nyesom Wike, gwamnan jhar Rivers.
Yace:
"Na yi niyyar mayar da Najeriya kasa guda cikin kasashe mafi karfin tattalin arziki a duniya. Na ce al'ummar kudu maso gabas ya kamata a baiwa tikiti saboda Igbo sun dade sun goyon bayan wasu. Saboda yanzu banda wata manufa illa in janye daga takara kuma in goywa Nyesom Wike baya."

"Ina umurtan dukkan magoya baya na su dangwalawa Wike."

Rahoton Punch

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya dira wajen zabe, jama'a sun kwale da ihu

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya dira wajen zaben fidda gwani.

Wike ya isa filin kwallon MKO Abiola ne misalin karfe 5:30 na yamma.

ChannelsTV ta dauki bidiyonsa lokacin da ya isa wajen:

Yanzu-yanzu: Jami'an hukumar EFCC sun dira wajen zaben fidda gwanin PDP

Wasu jami'an hukumar hana almundahana da yiwa arzikin kasa zagon sun dira farfajjiyar filin kwallon MKO Abiola, inda PDP ke gudanar da zaben fidda gwanin dan takaran shugaban kasa.

Punch ta ruwaito cewa jami'an sun dira misalin karfe 4:40 na yamma amma babu wanda ya san abinda ya kawo su.

Atiku, Wike, Saraki: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau
Atiku, Wike, Saraki: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau Hoto: MobilePunch
Asali: Twitter

Atiku ya dira wajen zabensu

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya dira farfajiyar gudanar da zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP.

Atiku a zaben 2019 ne ya lashe zaben fidda gwanin, wannan karon ko zai kai labari?

Deleget din Kano sun dira wajen zabe, sun ce sai Wike

Deleget daga gida jihar Kano sun dira farfajiyar velodrome na filin kwallon MKO Abiola don musharaka a zaben fidda gwanin yan takaran shugaban kasa a zaben 2023.

Deleget din na sanye da hulunan Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, kuma akan ji wasu na ihun ''Wallahi sai Wike"

Kalli bidiyon da Daily Trust ta dauka:

Komai ya kankama, Jami’an tsaro da Deleget sun fara dira

Atiku, Wike, Tambuwal: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau
Atiku, Wike, Tambuwal: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau
Asali: Facebook

Atiku, Wike, Tambuwal: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau
Atiku, Wike, Tambuwal: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau Hoto: tvcnewsng
Asali: Facebook

Atiku, Wike, Tambuwal: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau
Atiku, Wike, Tambuwal: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau Hoto: tvcnewsng
Asali: Facebook

Atiku, Wike, Tambuwal: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau
Atiku, Wike, Tambuwal: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau
Asali: Facebook

Tun kan a fara, dan takara kujerar shugaban kasa, Muhammad Hayatudeen, ya janye

Tun kan a fara, dan takara kujerar shugaban kasa, Muhammad Hayatudeen, ya janye daga takarar.

Hayatudeen ya aike wasika wa Shugaban uwar jam’iyyar, Iyorchia Ayu, riwayar Vanguard

Ya bayyana cewa dalilin takararsa shine yadda aka mayar da harkar ta kudi kawai babu mutunci.

A wasikar yace,

”Ban shiga siyasa da neman shugabancin kasa don son kai na ba ko son mulki, amma kawai na shiga ne don yiwa kasar nan bauta.”
”Bayan shawari da nayi, na yanke shawarar janyewa saboda yadda aka kudintar da lamarin.”

Atiku, Wike, Tambuwal: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau
Atiku, Wike, Tambuwal: Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin PDP ke gudana a yau
Asali: Facebook

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng