Da duminsa: Abba, dan gidan Gwamnan jihar Kano, ya zama dan takarar majalisar wakilai, kowa ya janye masa

Da duminsa: Abba, dan gidan Gwamnan jihar Kano, ya zama dan takarar majalisar wakilai, kowa ya janye masa

  • Daya daga cikin 'yayan Gwamnan jihar Kano ya samu sahalewar yan yankinsa don zama dan takaran APC
  • Abba wanda akafi amfani da sunansa wajen wakar kamfen Ganduje a 2019 zai nemi kujerar majalisar wakilai
  • Sanata Barau Jibrin da wasu jiga-jigan siyasar Kano ta Arewa ne suka yanke wannan shawarar

Kano - Injiniya Umar Abdullahi Ganduje wanda aka fi sani da Abba kuma dan gidan Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje ya zama dan takarar majalisar wakilan tarayya.

Abba na niyyar wakiltar mazabar Dawakin Tofa, Rimingado da Tofa

Hadimin gwamnan jihar kan kan kafofin yada labaran zamani, Abubakar Aminu Ibrahim, ya sanar da cewa wanda ke neman kujerar a baya ya janyewa Abba.

A cewarsa, sun yanke wannan shawara ne a wata zama da suka yi da daren Alhamis.

Kara karanta wannan

APC tayi zazzaga a jihar Arewa, fitattun ‘Yan Majalisa 7 za su rasa kujerunsu a 2023

Yace:

"A daren wannan rana ta Alhamis, 26 ga watan mayu 2022, Dr. Junaidu Yakubu me neman takarar Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Dawakin Tofa, Rimingado da Tofa ya janyewa Engr. Umar Abdullahi Ganduje Takararsa a zaben fitar da gwani na Jamiyyar APC da za'ayi a gobe insha Allah.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Anyi wannan zaman ne a bisa Shugabancin Sanatan Kano ta Arewa Barau I. Jibrin da Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Bichi, Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi.
Taron ya samu Halartar Shugabannin Kananan Hukumomin Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa, Kwamishinonin wannan yanki da Dattijan Jamiyyar APC na wannan yankin."

Abba, dan gidan Gwamnan jihar Kano
Da duminsa: Abba, dan gidan Gwamnan jihar Kano, ya zama dan takarar majalisar wakilai, kowa ya janye masa Hoto: Gandujiyya Online
Asali: Facebook

Surukin Ganduje ya lashe zaben takarar ‘Dan Majalisa

A wani labarin kuwa, Idris Abiola-Ajimobi, wanda ‘da ne a wajen Marigayi Abiola Ajimobi shi ne ‘dan takarar jam’iyyar APC a mazabar Kudu maso yammacin Ibadan.

Kara karanta wannan

Tikitin shugaban kasa na PDP: Ina addu’a Allah yasa Wike ya kai labari – Okezie Ikpeazu

Premium Times ta ce Idris Abiola-Ajimobi ne ya yi nasara a zaben fitar da gwanin da jam’iyyar APC ta shirya na kujerar ‘yan majalisu a ranar Alhamis.

Idris Ajimobi zai rikewa APC tuta a yankin Kudu maso yammacin Ibadan a zabe mai zuwa.

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta rahoto cewa ‘yan takarar wannan kujera ta majalisar dokoki sun janye, sun ba Ajimobi damar takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: