Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau

Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau

Jam'iyyar APC a Najeriya, a yau Alhamis, 26 ga Mayu, 2022 take gudanar da zaben fidda gwanin yan takaran gwamna a zaben 2023.

Za'a gudanar da wannan zabe ne a jihohi 32 a fadin tarayya.

Ku bibiyi shafin nan don samun bayanai kai tsaye kan zabuka.

Umar Bago ya lashe zaben fidda dan takarar gwamnan APC a Neja

Umar Mohammed Bago ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani na takarar kujerar gwamnan jihar Neja a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress(APC), jaridar The Nation ta rahoto.

Bago wanda ya kasance dan majalisa mai wakiltan mazabar Chanchaga a majalisar wakilai ta tarayya ya kayar da yan takara tara a zaben.

Air Marshal Abubakar Saddique ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan jihar Bauchi

Air Marshal Abubakar Saddique a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan jihar Bauchi na jam’iyyar APC.

Sanarwar na zuwa ne jim kadan bayan kammala kada kuri'u da deliget-deliget na APC suka yi a zaben fidda gwanin da ya gudana a jihar.

Tsohon Sojan yanzu zai kara da tsohon sakataren gwamnan jihar Bauchi na PDP a 2023

Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau
Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau
Asali: UGC

Tsohon Kwamishanan INEC ya kayar da mataimakin gwamna, ya lashe zaben fidda gwanin APC a Plateau

Yilwatda Nentawe, tsohon REC na hukumar zabe INEC, ya lallasa mataimakin gwamnan jihar Plateau, Sonni Tyoden, a zaben fidda gwanin APC.

Shugaban kwamitin zaben, Habu Ajiya, ya sanar da hakan da safiyar Juma'a.

Nentawe ya samu kuri'u 803.

Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau
Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau Hoto: TheCable
Asali: Facebook

Aisha Binani ta lallasa mazaje biyar, ta lashe zaben fidda gwanin APC a Yola

Sanata Aishatu Binani ta kayar da maza biyar a zaben fidda gwanin yan takaran gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa.

Shugaban kwamitin zaben, Gamba Lawan, yayin sanar da sakamakon ya bayyana cewa Binani ta samu kuri'u 430, inda Nuhu Ribasu ya samu 288.

Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau
Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau Hoto: ChannelsTV
Asali: Twitter

Bayan harbe mutum daya, an dakatad da zaben fidda gwanin jihar Taraba

Kwamitin gudanar da zaben fidda gwanin jam'iyyar APC a jihar Taraba ta dakatad da zaben sai baba ta gani bisa sabanin dake tsakanin yan takaran da salon da za'a bi wajen gudanar da zaben.

Shugaban kwamitin, Lawrence Onuchukwu, ya ce bayan harbe daya daga cikin mambobinsa da aka yi, kwamitin ta fuskanci kalubale da dama wanda ya zama wajibi a magancesu kafin a iya gudanar da zaben, rahoton TheNation.

Ya bayyana hakan ne a hedkwatar yan sanda jihar dake Jalingo.

An dage zaben fidda gwani a jihar Oyo

An dage zaben fidda gwanin jihar Oyo zuwa yammacin Juma'a.

NAN ta ruwaito cewa kwamitin zaben karkashin jagorancin Tokunbo Afikuyomi, suka sanar da hakan.

Bayan kwashe sa'o'i ana jira a fara zaben, sanarwar tace an dage ne saboda na gano wasu wadanda ba Deleget ba suka cika farfarjiyar a Ibadan.

Wadanda ke takara a zaben sun hada da Teslim Folarin, Adebayo Adelabu, Niyi Akintola (SAN), Azeez Adeduntan, Akeem Agbaje da Hakeem Alao.

Na hannun daman Amaechi ya lashe zaben jihar Rivers

Shahrarren dan kasuwa, Tonye Cole, ya lashe zaben fidda gwanin jam'iyyar All Progressives Congress APC a jihar Rivers.

Cole ya kayar da sauran yan takaran kuma shi zai wakilci jam'iyyar a 2023.

Ya samu kuri'u 986 yayinda Ojukaye Flag Amachree, Seconte Davies, Ibinabo West, da Benrard Mikko dake biye da shi suka samu kuri'u 190, 47, 43 da 2 a jere.

Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau
Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau
Asali: Depositphotos

An damke yaran siyasan Aisha Binani suna rabawa Deleget makudan kudi a Adamawa

An damke wasu yan siyasa biyu da ake zargin masu yiwa Sanata Aisha Binani yakin neman zabe ne suna rabawa Deleget makudan kudi a jihar Adamawa.

An tattaro cewa Sanatar ta yiwa Deleget alkawarin basu ninkin duk kudin da sauran yan takara suka basu.

Tana cikin masu takarar neman gwamnan Adamawa karkashin APC.

Labarai kai tsaye
Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Zulum ya ci zaben fidda gwani

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihaar Borno ya yi nasara a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da aka yi a birnin Maiduguri da aka yi a yau Alhamis.

Maigari Ahmadu, shugaban zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da majalisar jihar Borno, ya sanar da Zulum a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri'u 1,411.

Ya yi bayanin cewa, an saka kuri'u 1,560 wadanda suka yi rijistar zaben fidda gwanin yayin da aka tantance kuri'u 1,411.

Gwamnan Legas ya lashe zaɓen fidda gwanin APC

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC, ya zama ɗan takarar gwamna a zaɓen 2023, kamar yadda Punch ta ruwaito.

An bayyana gwamnan a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen fitar da ɗan takarar gwamnan Legas karkashin APC wanda ya gudana a Mobolaji Johnson Sport Arena, Onikan, jahar Legas.

Yanzu zai kara d Jide Jandor na jam'iyyar PDP.

An yi garkuwa da 'yar takarar APC ana tsaka da zaben fidda gwani

Yar takara a karkashin jam'iyyar APC da ke hararo yin wuf da tikitin mazabar Qua'an Pan ta kudu da ke jihar Filato a zaben 2023, Honarabul Na'anyil Magdalene, an yi garkuwa da ita.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Ubah Gabriel, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace kwamishinan 'yan sanda ya tura runduna ta musamman domin ceto ta, rahoton Daily Trust.

An sace Magdalene a ranar da ake yin zaben fidda gwani na jam'iyyarta.

Gwamna Abdullahi Sule ya lashe zaben fidda gwani a Nasarawa

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasawara ya lashe zaben fitar da gwani kuma shi zai wakilci APC a zaben 2023.

Gwamnan ya lallasa abokiyar hamayyarsa, Dr Fatima Abdullahi, uwargidar Shugaban uwar jam'iyyar APC.

Ya lashe dukkan kuri'u 735 ya bar mata 0.

Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau
Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau
Asali: Facebook

Gwamna Inuwa na Gombe ya lashe zaben fidda gwani

Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya zama dan takaran gwamnan jihar Gombe a zaben 2023.

Shugaban kwamitin zaben, Dr Abdullahi Dabo, ya sanar da hakan ranar Alhamis a inda aka taru don gudanar da zaben, rahoton Daily Trust.

Yace Gwamna Inuwa ya lashe zaben saboda shi kadai ya sayi Fom din takara kuma shi kadai aka tantance.

Gwamna Inuwa yanzu zai fafata da Muhammad Jibril Barde na jam'iyyarPeoples Democratic Party (PDP), da sauran jam'iyyun da zasu fito a 2023.

An hana abokin hamayyar Gwamnan Legas shiga farfajiyar zaben fidda gwani

Kwamitin gudanar da zaben fidda gwanin gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress APC a yau Alhamis ta hana daya daga cikin yan takaran shiga filin kwallon Teslim Balogun dake Surulere, inda ake gudanar da zaben.

Punch ta ruwaito cewa Mustapha yace an hanasa shiga da sunan cewa ba'a tantancesa ba.

Mustapha, ya sayi Fom din N50m bayan murabus daga kujerarsa na sakataren din-din-din ma'aikatar ma'adinai da makamashi a Legas.

Jam'iyyar APC
Labarai kai tsaye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau Hoto: Mobile Punch
Asali: Facebook

Gwamna Zulum, Mai Mala Buni da AbdulRahman basu da abokan hammaya, sun lashe zabe tun kan a fara

Da farko dai tun kan a fara zaben fidda gwanin, gwamnoni uku basu da abokan hamayya a wannan zabe.

Hakan na nufin cewa kai tsaye sun lashe zaben kuma su zasu wakilci jam'iyyar APC a zaben 2023.

Gwamnonin sun hada da;

  1. Farfesa Babagana Umara Zulum na jihar Borno
  2. Mai Mala Buni na jihar Yobe,
  3. AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara

Jam'iyyar APC
Labarai kan tsakye kan yadda zaben fidda gwanin Gwamnonin jam'iyyar APC ke gudana yau Hoto: APC
Asali: Facebook

Online view pixel