Kano: Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kwankwaso da wasu biyu sun fice daga NNPP, sun koma APC
- Yayin da kowace jam'iyya ke shirin tunkarar zaɓen 2023, siyasar Kano na ɗaya daga cikin wacce ta fi jan hankali a Najeriya
- Wasu mambobin majalisar jihar Kano da suka haɗa da mai wakiltar mazaɓar Kwankwaso wato Madobi sun fice daga NNPP sun koma APC
- Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan sanatan Kano ta tsakiya, Malam Shekarau, ya koma NNPP
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - Ɗan majalisar jiha mai wakiltar mazaɓar tsohon gwamna, Rabiu Kwnakwaso wato Madobi, Honorabul Kabiru Yusuf Isma’il, ya fice daga jam'iyya mai kayan marmari NNPP ya koma APC.
Yan majalisun sun sauya sheka ne kwanaki kaɗan bayan jam'iyyar APC ta rsa babban jigonta kuma sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam'iyyar NNPP mai tashe musamman a Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, shi ne da kansa ya tarbi Malam Shekarau, ya miƙa masa tikitin Sanata.
Sauran yan majalisu da suka sauya sheƙa zuwa APC
A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya fitar ya ce mamba mai wakiltar mazaɓar Dawakin Kudu, Honorabul Mu’azzam El-Yakubu, ya fice daga jam'iyyar Kwankwaso, ya koma APC.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kwamishinan ya ce guguwar sauya sheƙa ya afka cikin sansanin jam'iyyar NNPP musamman yan majalisun jiha da kuma na tarayya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Malam Garba ya ce dama tuni mamba mai wakiltar mazaɓar Bagwai/Shanono a majalisar dokokin jihar Kano, Isa Ali, ya sake komawa APC bayan da farko ya koma NNPP.
Ana cigaba da samun masu sauya sheka daga wannan jam'iyya zuwa wata jam'iyya a faɗin jihar Kano yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2023.
A watan da ya gabata, yan majalisa 14 a majalisar jihar Kano suka fice daga PDP zuwa jam'iyyar NNPP mai kayan marmari, wasu kuma sun koma APC kwanaki kaɗan bayan sun fita.
A wani labarin na daban kuma Sanata Ekweremadu ya janye daga zaɓen fidda gwani na PDP, zai koma APC
Sanata Ike Ekweremadu, ya janye daga shiga a dama da shi a zaben fidda gwani na yan takarar gwamnan jihar Enugu a PDP.
Wasu bayanai sun nuna cewa tsohon shugaban majalisar dattawan na shirin ficewa daga PDP kuma da yuwuwar APC zai nufa.
Asali: Legit.ng