2023: Shahararren Mawakin Najeriya ya yi nasarar samun takarar ‘Dan Majalisa a PDP
- Jam’iyyar PDP za ta tsaida Olubankole Wellington a matsayin ‘dan takararta a mazabar Eti-Osa
- Olubankole Wellington watau Banky W zai gwabza da wanda APC ta ba tikiti a takarar ‘dan majalisa
- Banky W ya yi suna wajen harkar waka da yin fim, ya shiga siyasa da nufin kawo sauyi a Najeriya
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Lagos - Fitaccen mawakin nan ‘dan kasar Najeriya da kuma Amurka, Olubankole Wellington, wanda aka fi sani da Banky W ya samu tikiti a PDP.
Vanguard ta kawo rahoto a ranar Litinin 23 ga watan Mayu 2022 da ya tabbatar da cewa Mista Olubankole Wellington zai yi takara a jam’iyyar PDP.
Banky W shi ne wanda ya lashe zaben fitar da gwani na kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya na mazabar Eti-Osa a jihar Legas da PDP ta gudanar.
A karshen makon da ya gabata ne jam’iyyar PDP ta shirya zabukan tsaida gwani domin fitar da wadanda za su yi mata takarar majalisa a zabe na 2023.
Mawakin yana cikin wadanda suka samu nasara a kan abokan hamayyarsu a jam’iyyar adawar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Premium Times ta ce Wellington ya ci kuri’a 28, don haka aka tabbatar da shi a matsayin wanda zai rikewa jam’iyyar hamayyar tuta a mazabar Eti-Osa.
Wannan ne karo na biyu
Idan za a tuna, Tauraron mawakin ya nemi wannan kujera a zaben 2019 a karkashin sabuwar jam’iyyar Modern Democratic Party da aka kafa a 2017.
Mista Wellington ya sha kashi ne a hannun ‘dan takaran da APC ta tsaida, Babajide Obanikoro.
Kwanakin baya sai mawakin ya bada sanarwar cewa ya fice daga jam’iyyar MDP, ya koma PDP da nufin takara a babbar jam’iyya a zaben shekarar badi.
Wanene Banky W?
Shekaru kimanin 40 da suka wuce aka haifi Olubankole Wellington a kasar Amurka. Wannan ya sa mawakin ya zama yana da shaidar zama 'Dan Amurka.
Bayan dawowarsa Najeriya ya fara wake-wake tun yana karami a coci. Daga baya Banky W ya gawurta, har ya zama yana cikin fitattun mawaka a yau.
Akwai masu takarar bogi a APC
Dazu aka ji labari Kayode Fayemi ya ziyarci jihar Neja da nufin samun kuri’un ‘yan APC a zaben fitar da gwani na takarar shugabancin Najeriya a 2023.
Tsohon Ministan ya yarda an gagara gyara wuta da inganta tsaro, ya sha alwashin zai magance matsalolin kasar, ya ce shi da gaske yake takara a APC.
Asali: Legit.ng