Abinda ya kamata ka sani game da mutum 23 ke son gadon Buhari karkashin APC
Bayan jeka-ka-dawo da yan siyasa suka yi na sayan Fom din takara karkashin jam'iyya mai ci ta All Progressives Congress (APC), mutum 23 kadai suka cike Fom din kuma suka mayar.
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Amma har yanzu ana tattaunawa shin wa jam'iyyar ta APC za ta baiwa tikitin takara kujerar shugaban kasa.
Shin me yasa mutane da yawa ke neman zama shugaban kasa? Wai me suke so ne? Shin kujerar shugaban kasa ta zama ta kowani irin mutu? Shin don son kasa sukeyi ko son kawunansu? Shine mutum nawa cikinsu zasu iya mulkar kasa irin Najeriya?
Amma yanzu an zo wajen, za'a tantance yan takara kuma saura kwanaki goma zaben tsayar da gwani.
Ga jerin mazaje 22 da mace daya dake neman kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC:
1. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Tsohon gwamnan jihar Legas (1999-2007)
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
2. Yahaya Adoza Bello
Gwamnan jihar Kogi (2016 - yanzu)
3. Dave Umahi
Gwamnan jihar Ebonyi (2015- yanzu)
4. Emeka Nwajiuba
Karamin Ministan Ilimi (2019 -2022)
5. Chibuike R. Amaechi
Kakakin majalisar dokokin jihar Rivers (1999-2007), Tsohon gwamnan jihar Rivers (2007-2015), Ministan Sufuri (2015-2022).
6. Fasto Nicholas Felix
Fasto mazauni kasar Amurka
7. Farfesa Yemi Osinbajo
Tsohon Fasto kuma Mataimakin shugaban kasa (2015- kawo yanzu)
8. Ken Nnamani
Tsohon Shugaban majalisar dattawan Najeriya
9. Fasto Tunde Bakare
Tsohon abokin takaran Shugaban Buhari a 2011 kuma Faston Latter Rain Assembly
10. OlaDimeji Bankole
Tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya (2007-2011)
11. Rochas Okorocha
Tsohon gwamnan jihar Imo (2011-2019), Sanata mai wakiltan Imo ta yamma (2019-yanzu)
12. Ibikunle Amosun
Tsohon gwamnan jihar Ogun (2011-2019),Sanata mai wakiltan Ogun ta tsakiya (2019-yanzu)
13. Sanata Robert Ajayi Boroffice
Sanata mai wakiltar Ondo ta Arewa (2011 - yanzu)
14. Ogbonnaya Onu
Ministan Kimiya da fasaha (2015 - 2022)
15. Benedict Ayade
Gwamnan jihar Cross Rivers (2015-yanzu)
16. Ahmad Ibrahim Lawan
Tsohon dan majalisan wakilai (1999–2007), Dan majalisan dattawa (2007-yanzu), Shugaban majalisar dattawa (2019-yanzu)
17. Ikeobasi Mokelu
Tsohon Ministan Labarai da al'adu lokacin gwamnatin mulkin soja n Janar Sani Abacha
18. John Kayode Fayemi
Gwamnan jihar Ekiti (2010-2014), Ministan ma'adinai (2015-2018), Gwamnan jihar Ekiti karo na biyu (2018-yanzu).
19. Mrs. Uju Kennedy
20. Abubakar Badaru Talamiz
Gwamnan jihar Jigawa (2015-yanzu)
21. Godswill Akpabio
Gwamnan jihar Akwa Ibom (2007-2015), Sanata (2015-2019), Ministan Neja Delta (2019-2022)
22. Ahmad Sani Yarima
Tsohon gwamnan jihar Zamfara (1999-2007), Sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma (2007-2019)
23. Tein Jack-Rich
Shugaban kamfanin Belemaoil Producing Limited
Asali: Legit.ng