Gwamna Abubakar Bello ya rantsar da sabbin kwamishinoni a jihar Neja

Gwamna Abubakar Bello ya rantsar da sabbin kwamishinoni a jihar Neja

  • Gwamna Bello na jihar Neja ya rantsar da sabbin kwamishinoni Bakwai biyo bayan aje aikin masu neman takara
  • Bello ya roke su da su tashi tsaye wajen kokarin sauke nauyin da aka ɗora musu musamman a irin wannan lokacin me kalubale
  • Ya ce babu wani isasshen lokaci yayin da wa'adin gwamnatin ke gab da ƙarewa, don haka su miƙe tsaye su taimaka masa

Niger - Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya rantsar da sabbin kwamishinoni Bakwai a majalisar zartarwar jihar Neja biyo bayan murabus ɗin na baya da zasu tsaya takara.

Da yake jawabi a wurin bikin rantsarwa a fadar gwamnatinsa da ke Minna, Bello ya nemi su tashi tsaye wajen sauke nauyin da Allah ya ɗora musu, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Batanci: Ku girmama addinin mutane da abinda suka yi imani da shi sai a zauna lafiya, El-Rufa'i

Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja.
Gwamna Abubakar Bello ya rantsar da sabbin kwamishinoni a jihar Neja Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

A jawabinsa, gwamna Bello ya ce:

"Mun zaɓe ku ne bayan samun rahoton kwazon kowane ɗaya daga cikin ku. Matakin mu na zakulo ku da sanya ku cikin gwamnati ya biyo bayan kyakkywan yabon da muka samu game da ku."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bello ya bayyana yaƙininsa cewa sabbin kwamishinonin za su kara wa gwamnatin martaba a ragowar yan watanni da suka rage.

Gwamnan ya kuma roki kwamishinonin su zage dantse wajen aikin da aka sanya su yadda ya dace, inda ya ƙara da cewa sun shigo gwamnati a lokacin da ayyukan gwamnati ke kara faɗi.

"A lokacin da kalubale suka ƙaru wanda hakan na nufin babu wani isasshen lokaci da zaku nuna banbanci."

Jerin sabbin kwamishinonin da Bello ya rantsar

Sabbin kwamishinonin sun haɗa da, Abraham Umar, Habila Galadima, Usman Tinau, Kabiru Abbas, Yusuf Gunu, Sani Lafiya da Emmanuel Musa, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta jero sharudan da za su sa a hana mutum takara a 2023 bayan ya saye fam

NAN ta rahoto cewa Alƙalin alƙalai na jihar Neja, Mai Shari'a Halima Abdulmalik, wacce ta samu wakilcin Mai Shari'a Bilkisu Yusuf, ita ce ta bai wa sabbin kwamishinonin rantsuwar kama aiki.

A wani labarin kuma Gwamna Ganduje ya kalli idon ministan Buhari mai murabus, ya ƙi goyon bayan ya gaji shugaban ƙasa a 2023

Gwamna Ganduje na jihar Kano ya ƙi ayyana goyon bayansa ga tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yayin da ya kai masa ziyara a Kano.

A jawabin Amaechi, ya bayyana cewa ya san inda akalar gwamnan ta dosa game da wanda yake so ya gaji Buhari a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: