Gwamna Ganduje yaƙi goyon bayan Ministan Buhari ya zama shugaban ƙasa a 2023
- Gwamna Ganduje na jihar Kano ya ƙi ayyana goyon bayansa ga tsohon ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yayin da ya kai masa ziyara a Kano
- A jawabin Amaechi, ya bayyana cewa ya san inda akalar gwamnan ta dosa game da wanda yake so ya gaji Buhari a 2023
- Tsohon gwamnan Ribas ɗin ya zayyano wasu dalilai da a cewarsa sun isa su tabbatar da ya fi kowa dacewa da zama shugaban ƙasa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Kano - Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahu Umar Ganduje, ya ƙi goyon bayan tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya gaji kujerar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Daily Trust ta ruwaito cewa Mista Amaechi, wanda ya aje aikinsa a majalisar zartarwar shugaba Buhari domin cika burinsa na zama shugaban kasa, ya kai ziyara Kano ranar Laraba.
A wurin taronsa da Ganduje da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC, gwamnan ya ce Kano, "Jiha ce mai lilo, kuma zata cigaba da zama a haka mai rabo ka ɗauka."
Ganduje ya kuma ƙara da cewa Amaechi da sauran yan takara za su san inda Kano ta karkata idan lokacin hakan ya yi, kamar yadda Punch ta ruwaito.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Nasan inda ka fi karkata - Amaechi
Tun farko, Amaechi ya faɗa wa gwamnan cewa mutanen da ke cikin APC sun san inda ya karkatar da goyon bayansa, amma ya zo Kano ne don ya gamsar da shi cewa ya fi kowa cancanta a cikin yan takara.
An yi amanna cewa Ganduje babban masoyin jagoran APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne, wanda yana ɗaya daga cikin masu hangen kujera lamba ɗaya a Najeriya.
Amaechi ya ce ya fi Tinubu cancanta saboda Tinubu bai taɓa ɗana kujerar Minista ba hakazalika bai shiga majalisa ba, tsohon gwamnan Legas ɗin ya rike kujerar siyasa ne na wani takaitaccen lokaci.
Ya ƙara da cewa ya zarce Yemi Osinbajo kwarewa saboda lokacin da Osinbajo ke kwamishina a Legas, tuni shi ya kai muƙamin kakakin majalisar jihar Ribas.
A cewarsa bayan haka ya kwashe wa'adin mulki biyu a matsayin gwamnan Ribas yayin da Osinbajo bai sake rike wani muƙami ba bayan kwamishina har sai da aƙa naɗa shi mataimakin shugaban kasa.
A wani labarin kuma Ministan albarkatun man fetur ya janye daga takarar shugaban kasa a 2023
Karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, ya janye daga takarar shugaban kasa ya koma bakin aiki.
Wata majiya daga ma'aikatar ta bayyana cewa ministan ya ɗauki matakin domin taimaka wa shugaba Buhari ya karasa wa'adinsa.
Asali: Legit.ng