Tambuwal da 'Yan siyasa 3 da za su shiga zaben 2023 da niyyar takarar kujeru 2 a lokaci 1
- Tuni an fara lissafin 2023, ‘Yan siyasa na ta faman lissafin yadda za su samu tikiti a jam’iyyunsu
- Akwai ‘yan siyasan da ake tunanin za su shiga takara biyu da dabara saboda gudun bacin-rana
- Daga cikin wadanda suke cikin wannan rukuni akwai wasu Gwamnoni uku da ke kan karagar mulki
Jaridar Legit.ng ta kawo jerin ‘yan siyasan da ake tunani sun yanki fam biyu, ko kuma akalla an yanki fam din shiga takara da sunansu a zabe mai zuwa.
1. Aminu Waziru Tambuwal
Kwanakin baya The Nation ta kawo rahoto cewa Kwamishinan ayyuka da gidaje na jihar Sokoto, Hon. Inu Bala Bodinga ya yanki fam din neman Sanata.
Ana zargin Bodinga ya saye fam da sunan Aminu Waziri Tambuwal ne. Idan Gwamnan bai samu tikitin shugaban kasa ba, to zai yi takarar Sanata a PDP.
Irin wannan dabara Gwamnan ya yi a zaben 2023 da ya rasa zaben fitar da gwani a 2019. Wannan karo zai iya takarar kujerar Sanatan Sokoto ta yamma.
2. Bala Mohammed
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani rahoton da Sahara Reporters ta fitar ya nuna Ibrahim Kashim ya ajiye kujerarsa na Sakataren gwamnatin jihar Bauchi, yana takarar gwamna.
Jaridar WikkiTimes ta bayyana cewa Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed zai maye gurbin Ibrahim Kashim idan bai samu takarar shugaban kasa ba.
A baya an ji Gwamnan yana cewa ko da bai yi nasara a zaben fitar da gwanin zama shugaban kasa a PDP ba, yana da wasu dabarun da yake da shi a 2023.
3. Ben Ayade
Ana kishin-kishin cewa Farfesa Ben Ayade ya sayi fam din takarar Sanata a karkashin jam’iyyar APC. Duk da haka, Gwamnan yana harin tutar shugaban kasa.
Punch ta ce Ayade ya saye fam mai lamba 9498. Gwamnan zai yi takara da Orim Martin Ojie wajen neman Sanata idan bai zama ‘dan takarar shugaban kasa ba.
Tun farko dai Gwamnan na Kuros Riba ya ce bai sa takarar shugaban kasa a ka ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba shi wannan shawarar da suka hadu.
4. Adams Oshiomhole
Duk da ya ayyana niyyar zama ‘dan takarar shugaban kasa a karkashin APC, rahotanni sun tabbatar da cewa Adams Oshiomhole ya na neman tikitin zama Sanata.
Tsohon gwamnan ya na sha’awar zama Sanatan Arewacin jihar Edo idan bai samu yadda yake so ba. A halin yanzu Francis Alimikhena ne yake rike da wannan kujera.
Jibrin ya koma NNPP
Bayan ficewarsa daga APC a makon jiya, kun ji labari cewa an ga Hon. Abdulmumin Jibrin dauke da kwandon kayan marmari a bainar jama’a da ya ziyarci jihar Kano.
Jibrin yana cikin tawagar da ta yi wa Madugun Darika kuma jagoran NNPP watau Rabiu Kwankwaso barka da zuwa garin Kano daga birnin Abuja ranar Juma'a.
Asali: Legit.ng