Ana kokarin bata min suna ne, ban karbi N200m wajen Jonathan ba, Gwamna Badaru

Ana kokarin bata min suna ne, ban karbi N200m wajen Jonathan ba, Gwamna Badaru

  • Gwamna Badaru na Jigawa ya karyata labarin cewa ya karbi daruruwan miliyoyi hannun Goodluck Jonathan
  • Gwamnan, wanda shima yana takara kujeran shugaban kasa ya ce ba shi da wata alaka da Jonathan
  • Majiyoyi na nuna cewa Goodluck Jonathan ya sauya sheka jam'iyyar All Progressives Congress (APC)

Dutse - Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya yi watsi da rahoton cewa ya karbi N200m hannun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan don saya masa Fom din takara karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Wata kafar yada labarai a farkon makon nan ta ruwaito cewa an baiwa Badaru N200m don sayawa Jonathan da kansa Fam din takara.

Amma a hira da jaridar Leadership a Dutse ranar Laraba, Gwamna Badaru ta bakin mai magana da yawunsa, Auwal Sankara, ya ce karya ne.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar shugaban kasa a APC ya bayyana gaban kwamitin tantance sanatoci bayan ya siya fom din N100m

A cewarsa:

"Idan ka karanta labarin, zaka fahimta cikin sauki cewa shaci-fadi ne kawai don bata min suna da na Jonathan."
"Wasu abokan siyasa na suka tara N350m kuma suka dauki N100m ciki don saya min Fam kuma suka ajiye sauran don kamfe."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Badaru ya kara da cewa ba shi da wata alaka ta siyasa da Jonathan sabanin girmamashi da yake yi don kasancewarsa tsohon shugaban kasa.

Gwamna Badaru
Ana kokarin bata min suna ne, ban karbi N200m wajen Jonathan ba, Gwamna Badaru Hoto: BAdaru

A kullun Buhari na kwana da tashi da talaka a ransa – Gwamna Badaru

Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na kwana da tashi da talaka a ransa.

Badaru wanda ya kasance shugaban kwamitin zaben fidda gwani na gwamnonin APC, ya bayyana hakan ne a yayin hira da Channels TV a shirin Politics Today.

Kara karanta wannan

Dokar kulle: Bishop Kukah ya yabawa matakin Tambuwal, ya karyata batun kai hari gidansa

Badaru ya ce:

“Shugaban kasa Buhari ya tafiyar da wannan gwamnati cikin tsoron Allah da kuma daidai iyawarsa. Kuma yana bacci da tashi da talaka a ransa; ta yaya zai inganta rayuwar talaka. Iya sanina kenan kuma saboda mutane za su ga gaskiyar abin da muke yi kuma su fahimci yanayin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng