2023: Moghalu Ya Lale N25m Ya Biya Kuɗin Fom Ɗin Takarar Shugaban Ƙasa a Jam'iyyarsa
- Farfesa Kingsley Moghalu, Tsohon mataimakin babban bankin Najeriya ya siya fom din takarar shugaban kasa a ranar Talata.
- Moghalu ya biya N25m ne lakadan a sakatariyar jam'iyyar ta ADC da ke birnin tarayya Abuja
- Farfesa Moghalu ya yi alkawarin kawar da matsalolin da ke adabar Najeriya a halin yanzu na tsaro, ilimi da tattalin arziki
Abuja - Tsohon mataimakin babban bankin Najeriya, CBN, Farfesa Kingsley Moghalu, a ranar Talata, ya shiga takarar shugabancin kasa a hukumance bayan siyan fom din takarar zabe na jam'iyyar ADC, kan N25m.
Vanguard ta rahoto cewa Moghalu ya shaidawa manema labarai a sakatariyar ADC na kasa a Abuja ya ce dole a cire kabilanci a zaben Najeriya idan ana son a cigaba.
Ya ce za a iya samun shugabannin masu nagarta a kowanne kabila da addinai, ya kara da cewa lokaci ya yi da kwararru da masanna masu kwarewa za su karbi jagorancin Najeriya.
Duk da haka, Moghalu ya ce ya kamata a bawa yankin da bata taba fitar da shugaban kasa ba damar yin hakan a shekarar 2023.
Ya yi alkawarin zai magance kallubalen da ake fama da su a bangaren tsaro, hauhawar farashin kayayyaki da bangaren ilimi.
Moghalu ya ce mataki na farko shine samar da tsaro ga kasar ta hanyar yi wa yan sanda garambawul ta kara adadin jami'an yan sandan da kashi 300 cikin 100.
Ya kuma ce zai tabbatar da cewa an kashe akalla kashe 20 cikin 100 na kasafin kudin Najeriya a bangaren ilimi domin kawo karshen yawan yajin aikin ASUU.
2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa
A wani rahoton, Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.
Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.
Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.
A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.
Asali: Legit.ng