PDP: Shugabannin jam'iyya na jiha da na kasa sun bai wa hammata iska a Kano

PDP: Shugabannin jam'iyya na jiha da na kasa sun bai wa hammata iska a Kano

  • A ranar Laraba, an gano yadda rikici ya barke tsakanin wakilan jam'iyyar PDP na Kano da wakilan jam'iyyar na kasa a jihar Kano yayin wata arangama
  • Manema labarai sun gano yadda lamarin ya auku tsakanin Dahiru Haruna da Idi Zare Rigo a masaukin baki na Tahir idan aka tarbi daya daga cikin wakilan jam'iyyar na kasa
  • Shugaban jam'iyyar na jihar, Shehu Sagagi ya bayyana yadda bayan tarbar bakon, ya bukaci lemo, hakan yasa suka tafi nemo masa, kafin su dawo sun tarar dashi a wani daki daban inda rikicin ya barke

Kano - Rikici ya barke a ranar Laraba tsakanin wakilan shugabannin jam'iyyar PDP na Kano da wakilan jam'iyyar na kasa a cikin jihar.

Daily Trust ta tattaro yadda rikicin ya barke a masaukin baki na Tahir, inda aka tarbi daya daga cikin wakilin jam'iyyar na kasa.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

PDP: Wakilan jam'iyya na Kano sun yi arangama da wakilin jam'iyya na kasa a Otal
PDP: Wakilan jam'iyya na Kano sun yi arangama da wakilin jam'iyya na kasa a Otal. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, daga bisani aka mika wakilan jihar Kano biyu, wani Dahitu Haruna; da Idi Zare Rogo ga 'yan sanda.

Shugaban jam'iyyar, Shehu Sagagi ya shaida yadda aka tarbi wakilin jam'iyyar na kasa ( mai suna Barista Ekwudile) a filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA), tare da kai shi masaukin bakin Tahir, amma shi (Ekwudile) ya shaidawa wanda ya tarbe shi yana bukatar lemo, hakan yasa suka fita nemo masa.

"Yayin da suka dawo da lemon, ba su gan shi a dakin ba, sai daga baya suka gano shi a daki mai lamba 811, inda rikicin ya barke," a cewarsa.

Game da abunda ya haddasa rikicin, ya ce bashi da tabbaci, zai iya zama saboda mutanen da suka ga Ekwudile dasu ne, wanda ya yi sanadiyyar rikici tsakanin Haruna da Rogo.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Haka zalika, ya kara da bayyana yadda wakilan jihar suka ki amincewa da shirin gudanar da taron gundumar a Otel, a maimakon sakateriyar jam'iyyar da dama da ake ta take dasu.

Ba a samu wayar kakakin 'yan sandan jihar, SP Haruna Kiyawa ba har zuwa lokacin da aka tattara labarin nan, amma an gano yadda aka mika wakilan PDP ofishin 'yan sanda na marabar Badawa.

Sagagi na daya daga cikin yaran gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya canza sheka daga jam'iyyar zuwa NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel