Shugaban ƙasa a 2023: Bamu yanke hukunci kan tsarin karba-karba ba, Adamu
- Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce har yanzun ba su ɗauki matsaya ba kan tsarin karɓa-karba
- Adamu ya ce duk da ya samu alfarmar zama shugaban jam'iyya na kasa amma yanke wannan hukuncin ya fi karfin kujerarsa
- Ya kuma kare matakin zabga miliyan N100m a matsayim Farashin Fom da cewa ko kaɗan ba su yi dana sani ba
Abuja - Shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi, yace jam'iyya mai mulki ba ta yanke hukunci kan yankin da zata ba tikitin takarar shugaban ƙasa ba gabanin zaɓen 2023.
Adamu ya yi magana kan tsarin karba-karban ne ranar Jumu'a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan gabatar da ɗan takarar APC a zaɓen Ekiti, Abiodun Oyebanji, ga shugaban kasa Buhari a Aso Villa.
Sanata Adamu ya ce matakin wane yankin ƙasa ne zai zaƙulo ɗan takara a APC ya zarce matsayinsa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Da yake amsa tambaya kan wane yanki ne zai fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen mai zuwa, Adamu ya ce:
"A yau na samu alfarmar zama shugaban jam'iyya na ƙasa, jam'iyyar ta zarce matsayina, ba ta ɗauki mataki kan lamarin ba a yanzu, kuma ba zan iya hasashen abin da zai iya kasancewa ba."
Da yuwuwar APC ta kai tikitin takara kudu
Sai dai matakin APC na canza masu rike da ofisoshinta na ƙasa tsakanin Arewa da kuma Kudu, shi ne ya yi sanadin ɗarewar Adamu a matsayin Ciyaman na ƙasa.
Tun kafin babban taron na ƙasa, Gwamna Malam El-Rufa'i na Kaduna, ya ce duk da APC ba ta fito fili ta bayyana yankin da zata ba takara ba, amma canza masu rike muƙamai wata alama ce ta inda tikitinta ya nufa.
Shugaban APC ya kuma kare matakin zuga kudin Fom ɗin takarar shugaban ƙasa, inda ya ce jam'iyyarsa ba ta yi dana sani ba, kamar yadda The Nation ta rahoto.
A wani labarin kuma Ana raɗe-raɗin sauya sheka, mataimakin gwamna da Kwamishinoni 10 sun yi murabus
Yayin da ake yaɗa jita-jitar sauya shekar Tambuwal bayan ya gana da Buhari, kwamishinoninsa 11 sun aje aikinsu.
Mataimakin gwamnan jihar Sokoto , Manir Ɗan'iya, ya sauka da kujerar kwamishinan kananan hukumomi.
Asali: Legit.ng