‘Ya 'yan APC sun tarawa 'Dan Majalisa N25m domin ya yi takara da Gwamna mai-ci a 2023

‘Ya 'yan APC sun tarawa 'Dan Majalisa N25m domin ya yi takara da Gwamna mai-ci a 2023

  • Wasu ‘Yan majalisar dokokin jihar Adamawa sun tarawa Abdurrazaq Namdas kudin sayen fam
  • Abdullahi Ahmed Manager, Abdullahi Umar Nyako da Alhassan Hammanjoda ne su ka hada N25m
  • ‘Yan siyasan su na gani lokaci ya yi da mutanen Ganye/Jada/Mayobelwa za su rike jihar Adamawa

Adamawa - ‘Yan majalisar APC a jihar Adamawa sun tara Naira miliyan 25 domin sayawa ‘dan takarar gwamna, Abdurrazaq Namdas fam a zaben 2023.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa ‘yan majalisar dokokin Adamawa da ke karkashin jam’iyyar APC sun tallafawa takarar Abdurrazaq Namdas.

Honarabul Namdas mai wakiltar mazabun Toungo, Ganye, Jada da Mayobelwa a majalisar wakilan tarayya ya na harin kujerar gwamna a Adamawa.

‘Yan majalisar dokokin da suka tara wannan kudi su ne Hon. Abdullahi Ahmed Manager, Hon. Abdullahi Umar Nyako da kuma Hon. Alhassan Hammanjoda.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: ‘Dan Majalisar Tarayya ya rasu kwatsam, ana shirin fara lissafin 2023

"Lokaci ya yi"

Hon. Alhassan Hammanjoda a madadin sauran abokan tafiyarsa ya yi kira ga sauran ‘yan majalisar dokokin su marawa Namdas baya ya zama gwamna.

Hammanjoda yake cewa mutanen yankunan Toungo, Ganye, Jada da Mayobelwa ba su taba rike kujerar gwamna a Adamawa ba tun bayan Bamanga Tukur.

Hon. Abdurrazaq Namdas
Hon. Abdurrazaq Namdas a taron APC Hoto: Abdurrazaq Namdas
Asali: Facebook

Alhaji Bamanga Tukur bai wuce watanni uku a kan mulki ba, sai sojoji su ka yi juyin-mulki a karshen 1983. A lokacin ne aka kifar da mulkin Shehu Shagari.

A cewar Hammanjoda, shekaru hudun nan da Honarabul Namdas ya yi a majalisar tarayya ya nuna shi ‘dan siyasa ne mai sha’awar kawowa al’umma cigaba.

Sanda ya wakilci Namdas

Rahoton ya ce wani hadimin ‘dan majalisar, Hussaini Sanda ya wakilce shi a wajen taron da aka shirya domin a saya masa fam din shiga takarar gwamna a APC.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadi wanda za a fifita a tsarin da aka dauko na fito da ‘Dan takarar 2023

Hussaini Sanda ya godewa wadannan ‘yan majalisa uku da kuma dattawan yankinsa da kuma ‘yan kungiyar magoya baya da duka suka taimaka da gudumuwarsu.

Hussaini Sanda shi ne babban hadimin Abdulrazaq Namdas a wajen harkokin majalisar tarayya.

Fam din Fintiri

A watan da ya wuce ne aka ji labari wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin jihar Adamawa, sun sha alwashin cewa za su sayawa Ahmadu Umaru Fintiri fam a PDP.

Shugaban majalisar dokokin Adamawa, Rt. Hon. Aminu Iya Abbas ya shaidawa manema labarai cewa Gwamna Fintiri ya dace ya zarce kan karagar mulki a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel