‘Yan siyasa 10 a Kudu da Arewacin Najeriya da sai inda karfinsu ya kare a kan takarar Tinubu

‘Yan siyasa 10 a Kudu da Arewacin Najeriya da sai inda karfinsu ya kare a kan takarar Tinubu

  • Shakka babu, Asiwaju Bola Tinubu ya na cikin ‘yan takarar da sai an yi da gaske za a iya doke su a zaben fitar da ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC
  • Bola Tinubu ya na tare da wasu manyan ‘yan siyasa da ke goyon bayan shi. Jaridar Daily Trust ta kawo wasu daga cikin masu marawa takararsa baya a 2023
  • Legit.ng Hausa ta tuntubi Hadimin gwamnan Legas, Jibril Gawat, wanda ya tabbatar mata da cewa wadanda Tinubu ne ya shigo da su siyasa, su na da yawa

Ga wasu cikin na hannun daman Bola Tinubu a jam’iyyar APC

1. Kashim Shettima

Tsohon gwamnan jihar Borno ya zama tamkar Darekta Janar na yakin neman zaben Bola Tinubu. Sanatan ya na ganin ya kamata a ramawa kura aniyarta a 2023.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi ya sauya sheka daga APC zuwa PDP

2. Dayo Adeyeye

Wani kusa a tafiyar Tinubu shi ne Sanata Dayo Adeyeye. Daily Trust ta ce shugaban kungiyar SWAGA ya na cikin masu tallata takararsa a duk fadin Najeriya.

Tsohon Ministan ya hakura da neman Gwamnan Ekiti saboda Tinubu ya zama shugaban kasa.

3. Abu Ibrahim

A Arewa kusan babu wanda yake da tsohuwar alaka da Bola Tinubu a siyasa irin Abu Ibrahim. Tsohon Sanatan na Katsina ya na goyon bayan a ba Tinubu tuta.

Abu Ibrahim yana cikin wadanda suka fara hada shugaba Buhari da ‘dan siyasar a zaben 2011.

4. Iyiola Omisore

Rahoton ya bayyana cewa sabon sakataren APC na kasa, Sanata Iyiola Omisore mutumin Tinubu ne. Omisore ya taimakawa Tinubu a zaben gwamnan Osun a 2018.

A lokacin Omisore ya na SDP, ya yi sanadiyyar da Gboyega Oyetola ya lashe zaben gwamna.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari ya yi nadin sababbin mukamai, ya canza shugabannin FMBN

Tinubu
Bola Tinubu a taro Hoto: @OfficialBAT
Asali: Facebook

5. Abdulmuin Jibrin

Tsohon ‘dan majalisar tarayya, Hon. Abdulmuin Jibrin shi ne Darekta-Janar na majalisar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu’s Support Groups Management Council.

6. Adeseye Ogunlewe

Sanata Adeseye Ogunlewe ya na cikin wadanda suka hakura su ka bi Bola Tinubu. Ganin yi masa adawa ba zai yiwu ba, tsohon Sanatan ya zama ‘dan a-mutunsa.

7. Rilwan Akanbi

Wani tsohon Sanata da ke cikin jirgin Bola Tinubu shi ne Rilwan Akanbi. Sanata Akanbi yana cikin jagororin SWAGA, kuma ana takama da shi a siyasa Yarbawa.

8. Abdulhakeem Alawuje

Kwamred Hakeem Alawuje wanda ke shugabantar tafiyar Disciples of Jagaban (DOJ) ya na cikin yaran Bola Tinubu. Tsohon sojan yana goyon bayan a ba sa takara.

9. Mutiu Kunle Okunola

Mutiu Kunle Okunola yana cikin ‘yan adawan da suka dawo masoyan Tinubu. A yau Okunola ya kafa Tinubu 2023 Non-Negotiable domin taya shi yaki a zaben 2023.

10. Abdullahi Umar Ganduje

Ba a kawo gwamnan na Kano a sahun yaran ‘dan siyasar, amma idan ana maganar masu mara masa baya daga Arewa maso yamma, akwai gwamna Ganduje.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tara duk shugabannnin Majalisan APC, sun yarda su mara masa baya a 2023

Sauran na kusa da Tinubu

Ragowar mutanen Bola Tinubu sun hada da Gwamna Babajide Sanwo-Olu, Gwamna Gboyega Isiaka Oyetola, da shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Sai kuma Hon. James Faleke wanda ya kafa kungiyar Tinubu Support Group (TSG), Sanata Solomon Adeola, da shugaban majalisar Legas, Mudathis Obasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng