Atiku ya kwadaitar da matasa, ya yi masu alkawari muddin ya samu mulki, su ma sun samu

Atiku ya kwadaitar da matasa, ya yi masu alkawari muddin ya samu mulki, su ma sun samu

  • Atiku Abubakar ya yi zama na musamman da kungiyoyin da ke goyon bayan takararsa a zaben 2023
  • Wazirin Adamawa ya yi wa matasa alkawari cewa zai buda masu hanyar da za a rika yi da su a siyasa
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce burinsa shi ne ya girka matasa, sai ya damka masu shugabanci

Abuja – Alhaji Atiku Abubakar ya na kokarin kwadaitar da matasa a game da burinsa na zama shugaban kasar Najeriya a zabe mai zuwa da za ayi a 2023.

A ranar Laraba, Daily Trust ta rahoto Atiku Abubakar ya na mai cewa burinsa na zama shugaban Najeriya, zai ba matasa damar rike madafan iko a kasar nan.

Wazirin na Adamawa ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya yi zama da wakilan kungiyoyin siyasan da ke goyon bayansa wajen zama shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Na cancanci gaje kujerar Buhari: Inji Amaechi ga jama'ar Katsina yayin wata ziyara

Wadannan kungiyoyi na magoya baya sun zauna da ‘dan siyasar ne a ranar Talata domin tsara yadda ‘yan PDP za su kada masa kuri’a a zaben fitar da gwani.

Haka zalika, kungiyoyin su na neman ganin yadda sauran ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP za su bi Atiku Abubakar domin ganin ya cin ma burin da ya dade yana da shi.

Da yake yi wa masoyan na sa bayani, ya yi kira ga matasa da su shiga siyasa gadan-gadan, kamar yadda aka fara damawa da shi tun ya na ‘dan shekara 30-da.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar da wasu magoya bayansa a Abuja Hoto: Atiku.org
Asali: Facebook

Na ba matasa dama a lokacin Obasanjo - Atiku

Jaridar ta rahoto Atiku ya na cewa a lokacin da yake rike da kujerar mataimakin shugaban kasar Najeriya, ya yi amfani da damarsa wajen ba matasa mukamai.

Alhaji Abubakar ya ce mutane masu kananan shekaru sun rike mukamai masu mihimmanci a gwamnatinsu wanda ta yi mulki tsakanin 1999 zuwa 2007.

Kara karanta wannan

2023: Amaechi ya fara neman shawarwari, ya ziyarci sarakunan Daura, Kano da Bichi

Matasa za su samu mulki a bayan Atiku

‘Dan siyasar ya ce idan har ya yi nasarar karbar kujerar shugaban kasa a shekara mai zuwa, zai girka matasa ta yadda ragamar shugabanci zai koma hannunsu.

Kamar yadda The Cable ta kawo labari, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ya ji dadin ganin yadda matasa su ke mara masa baya ya nemi mulkin kasa.

Burin Atiku, a cewarsa shi ne ya horas da matasa masu tasowa, sai ya mika masu shugabanci.

Masu neman takara sun kusa 40

A jiya ku ka ji cewa 'yan siyasa 35 sun shaidawa Duniya cewa za su nemi kujerar shugaban Najeriya a zaben 2023. Atiku Abubakar ya na cikin 'yan jam'iyyar PDP.

Masu neman takarar sun hada da mutane 18 a PDP, da kuma 12 APC. Daga ciki akwai mata 6 da maza kusan 30. Ana ganin su Atiku su na cikin 'yan gaba-gaba a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng