Wasu Jiga-Jigan PDP biyu da daruruwan mambobi sun sauya sheƙa zuwa NNPP a Oyo

Wasu Jiga-Jigan PDP biyu da daruruwan mambobi sun sauya sheƙa zuwa NNPP a Oyo

  • Wasu manyan jiga-jigan PDP a jihar Oyo sun ja dandazon masoyan su zuwa jam'iyyar NNPP mai kayan marmari
  • Ɗaya daga cikinsu, tsohon ɗan takarar gwamna, Mista Popoola, ya ce laimar PDP ta tsage kuna jam'iyyar ba zata iya katabus ba a Oyo
  • A cewar masu sauya sheƙan sun zaɓi dawowa NNPP ne somin su fafata kowane irin zaɓe kuma su ci nasara

Oyo - Dandanzon mambobin jam'iyyar PDP a jihar Oyo bisa jagorancin jiga-jigai biyu, Olopoeyan da Joshua Popoola, sun sauya sheƙa zuwa NNPP mai kayan marmari, ranar Litinin a Ibadan.

Masu sauya sheƙan sun samu kyakkyawar tarba daga wurin shugabannin NNPP na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Sakatare, Dipo Olayokun, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

NNPP ta yi babban kamu a Oyo.
Wasu Jiga-Jigan PDP biyu da daruruwan mambobi sun sauya sheƙa zuwa NNPP a Oyo Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Mista Olopoeniyan ya raba gari da gwamnan Oyo, Seyi Makinde, bisa zargin nuna masa halin ko inkula da kuma tsantsar ɓangaranci.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Amaechi da wasu jiga-jigan APC 4 da Osinbajo zai gwabza da su ya gaji Buhari

Ya kuma bayyana cewa tuni ya yi hannun riga da jam'iyyar PDP, inda ya ƙara da cewa ya samu wurin zama a jam'iyyar NNPP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A hasashensa, NNPP ta yi kwarin ƙafar da zata shiga kowane zaɓe tun daga sama har ƙasa a 2023 kuma zata ci nasara.

Jagoran siyasa a jihar Oyo ya kuma tuna zamansa da Gwamna Makinde, ya yi ikirarin cewa shi ya kawo gwamnan siyasa kuma zai iya canza labarin.

Meyasa suka zaɓi NNPP?

Da yake nasa jawabin, Mista Popoola, tsohon ɗan takarar gwamna a PDP, yace sun shigo NNPP ne domin su fafata a babban zaɓen 2023 kuma su ci nasara.

Ya ce:

"Laimar PDP ta tsage kuma jam'iyyar ta rushe a jihar Oyo, mu muka gina jam'iyyar kuma yanzun mun bar ta hannun Makinde."
"Mun zo nan domin mu tabbatar da komawa NNPP a hukumance kuma mu karbi katin zama mamba, kuna ganin yadda masoyan su ke tururuwar dawowa NNPP yau."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta ba APC mamaki, ta lashe kujerun Ciyamomi 21 da Kansiloli 226 a Adamawa

A wani labarin kuma Hotunan Katafariyar Gada Mai Hawa Uku da Ganduje Ke Ginawa a Kano, Babu Irinta a Faɗin Najeriya

Gwamnatin Kano na cigaba da aikin gada mai hawa uku a Shataletalen NNPC dake Anguwar Hotoro.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce suna sa ran kammala aikin zuwa watan Satumba, an raɗa wa Gadar 'Muhammadu Buhari Interchange'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: