Abin da ‘Yan Facebook da Twitter ke ta fada kan shirin takarar Osinbajo a zabe mai zuwa

Abin da ‘Yan Facebook da Twitter ke ta fada kan shirin takarar Osinbajo a zabe mai zuwa

  • Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya tabbatar da niyyar neman takara a zabe mai zuwa
  • Farfesa Yemi Osinbajo ya bada sanawar cewa ya na da burin zama magajin Muhammadu Buhari
  • Jim kadan da jin wannan labari a Najeriya, shafukan sada zumunta na zamani da-dama sun karba

A wannan rahoto, mun tattaro abin da jama’a ke fada a dandalin sada zumunta a kan takarar mai girma mataimakin shugaban na Najeriya.

Ga na mu nan. Mu na nan! Shugaban kasar gobe. @ProfOsinbajo #Starboy #OsinbajoDeclares

- Bello Shagari

‘Dan takarar da ya fi dacewa kenan. Mu na tare da kai dari bisa dari ‘yallabai. #OsinbajoDeclares

- Atilola Philipps

Osinbajo ya shiga gidan kowa; ya samu karbuwa a Sokoto, yadda aka yi na’am da shi a Akwa Ibom. ‘Dan takarar kwarai bai da aibu da abin zargi. Abin farin ciki ‘Yan Najeriya sun karbi maganar.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa: Yadda Farfesa Yemi Osinbajo zai ayyana shirin gaje kujerar Buhari a yau

- Inji @thereal_godfrey

Shi kuwa @jayythedope ya na ganin an fi bukatar Farfesa Yemi Osinbajo a cocin RCCG fiye da yadda ake da bukatar shi a kujerar shugaban kasa.

Ka da ka ci mana albasa da bakin ka

Dominic Ebi ya ce:

“Mu mutanen Kudu maso kudu mu na goyon bayan ka.”

Amma nan take wani Koko Blaq ya maidawa Dominic Ebi martani, ya ce idan zai yi magana, ya yi magana da yawun bakinsa ne da na danginsa kawai.

Wani ‘dan jarida mai suna Eniola Daniel ya ce:

Ya ce ya amsa kiran mutane, amma cewa Buhari mai kishin kasa ne, akwai tangarda. Sannan kuma ya ce yana son karasa abin da suka fara!!! Za a gyara bangaren shari’a.
Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo Hoto: @tolanialli
Asali: Twitter

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Osinbajo ya tara gwamnonin APC don shaida musu aniyarsa ta gaje Buhari

Farfesa, barka da ka yi shawara mai kyau na yin takara. Mun dade mu na jiran ka ayyana burin ka. Amma da yardar Ubangiji ba za ka yi nasara ba.

- Uncle Midetush

A shafinsa na Facebook, Habeebullah Abdulrasheed Anda ya rubuta:

“A ra’ayina, ya na da koshin lafiya, ya fahimci matsalar da ke damun kasar nan, za a iya cewa shi ne ya fi kowa dacewa a APC.”

Fejiro Johnson ya yi dogon sharhi, ya na yabawa Osinbajo. Ga wani bangare daga ciki:

“A wannan zamanin na fasaha, Yemi Osinbajo ya yi dabara da ya kaddamar da neman takararsa ta kafar sada zumunta. Baya ga shigan sakon wurare masu nisa, ya kuma karada shafukan sada zumunta da gidajen yada labarai.”

Shi dai Ibrahim Adam tambaye yake yi:

"Shin taken yakin neman zaben Osinbajo zai zama ‘canji’ ne ko ‘tazarce’."

Osinbajo v Tinubu

A yau aka ji cewa maganar takarar Yemi Osinbajo ta ba mutane mamaki, inda aka ji wasu su na cewa ba su yi tunanin haka za ta faru ba a jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Dokubo Asari ya caccaki Gwamnan PDP, ya ce takararsa a 2023 ba za ta kai labari ba

Malam Abdulhaleem Ringim ya ce

"Wannan karon ban cinka daidai ba, ban taba tunani Osinbajo zai yi takara yayin da Tinubu ya ke neman takara ba. Mulki bala'i ne."

An ji Sulaiman Yaro a Facebook ya na cewa:

"Watakila ya na tare da Tinubu ne. Amma har yanzu ina shakkar cewa Osinbajo zai yi takara tare da Jagaban."

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng