Wani na kusa da Buhari, ya shiga sahun masu neman yin takarar Shugaban kasa a APC
- Babu mamaki nan da ‘yan kwanaki kadan a ji labarin Ikeobasi Mokelu ya yanki fam a jam'iyyar APC
- Tsohon shugaban kungiyar ‘I Stand With Buhari’, na kasa, Cif Ikeobasi Mokelu ya na neman takara
- Mokelu ya na tare da Shugaban kasa, kuma sun rike mukami tare da shi a gwamnatin Sani Abacha
Anambra – Labari na zuwa cewa Ikeobasi Mokelu ya na niyyar yin takarar shugaban kasa a Najeriya, kuma zai tsaya ne a karkashin jam’iyyar APC.
Jaridar Punch ta ce Cif Ikeobasi Mokelu ya kammala shirye-shiryen tsaf na sayen fam din neman tikitin shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki a kasa.
Ikeobasi Mokelu ya na cikin kusoshin jam’iyyar APC a kudancin Najeriya, sannan ana ganin ya na cikin na-kusa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Idan rahoton da mu ka samu ya tabbata, za a ji Mokelu nan da ba da dadewa ba, ya lale makudan kudi domin sayen fam din shiga takarar shugaban kasa a APC.
Ana tunanin tsohon Ministan ya na tare da wasu masu rike da madafan iko a fadar shugaban kasa.
Alakar Mokelu da Buhari
Gabanin zaben 2019, a shekarar 2018 ne Mokelu ya kirkiro tafiyar nan ta ‘I Stand With Buhari’, kuma ya na cikin masu kai wa da komawa a fadar Aso Villa.
Yayin da Muhammadu Buhari ya shugabanci hukumar PTF a lokacin Janar Sani Abacha, Mokelu shi ne Ministan harkokin yada labarai a gwamnatin sojan.
Siyasar APC a jihar Anambra
Kafin nan, Cif Mokelu zai zauna da ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a mazabarsa ta Ubolo Unodu da ke garin Oraifite, a karamar hukumar Ekwusigo a jihar Anambra.
Sannan ‘dan siyasar zai tattauna da manyan jam’iyyar APC daga yankin kudu maso gabashin Najeriya domin shaida masu burinsa na neman shugabanci.
Tun a jiharsa ta Anambra, Mokelu zai iya samun cikas a APC domin akwai masu zuga tsohon Gwamna, Chris Ngige ya fito takara a karkashin jam’iyyar.
Yanzu haka Sanata Chris Ngige ya na cikin manyan Ministoci a gwamnatin Muhammadu Buhari.
Arewa sun ci rabonsu – Bode George
A gefe guda kuma, an ji cewa Olabode George ya sanar da shugaban PDP na kasa cewa ba zai yiwu a iya cin zabe yayin da ake fada a Jihohin Legas da Kano ba.
Sannan tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ya hakikance a kan dole wanda zai zama shugaban kasa ya fito daga kudancin Najeriya a zaben 2023.
Asali: Legit.ng