Mai magana da yawun bakin Jam’iyyar PDP ya ce Gwamnan APC ya nemi ya kashe shi
- Kwamred Chika Nwoba ya bada labarin wahalar da ya sha a lokacin da aka yi ram da shi kwanaki
- Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na reshen jihar Ebonyi ya ce har an nemi ganin bayan shi
- Gwamna David Umahi ne Chika Nwoba ya ke zargin cewa ya bada umarni su yi masa allura, ya mutu
Ebonyi - Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP a jihar Ebonyi, Kwamred Chika Nwoba ya tuhumi gwamna David Umahi da neman hallaka shi.
A ranar Talata, jaridar Punch ta rahoto Chika Nwoba yana cewa gwamnan na jihar Ebonyi ya kitsa wannan ne a lokacin da yake tsare a hannun hukuma.
Gwamnatin jihar Ebonyi ta kama Nwoba kwanakin baya har ya shafe tsawon makonni hudu a tsare. Bai kubuta ba sai a farkon watan Maris da ya wuce.
An zargi mai magana da yawun bakin jam’iyyar PDP mai hamayya na Ebonyi da laifin yada karya a shafukan sada zumunta da kuma damfara ta yanar gizo.
A cewar Chika Nwoba, wadanda suke rike da madafan iko a Ebonyi sun yi yunkurin ganin bayan shi. A karshe manyan jami’an tsaro a Abuja suka cece shi.
Kwamred Nwoba ya kuma bayyana cewa a lokacin da ya shiga hannu, ‘yan sandan da ya kamata su ba shi kariya, sun zama tamkar hadiman gwamnan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
‘Dan adawan ya ce jami’an ‘yan sandan sun rika karbar umarni ne daga gwamnan Ebonyi, Umahi. CP Aliyu Garba ya yi alkawarin zai maidawa PDP martani.
Jaridar ta ce Nwoba ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya zanta da manema labarai a Litinin. An yi wannan zama ne a garin Abakaliki na jihar Ebonyi.
Bayan ya shiga hannu ya fito, Nwoba ya bayyana cewa akwai mutanen jihar Ebonyi barkatai da su ke tsare a ragar ‘yan sanda ba tare da dalilin kirki ba.
‘Dan siyasar ya ce bai samu matsala a gidan gyaran hali na Afikpo ba. Amma ya fahimci akwai mutanen jihar birjik da suke tsare saboda sabanin siyasa.
Kamar yadda ya fada, burin wadanda suka sace shi, shi ne su yi masa allura da magani domin ya mutu a bisa umarnin gwamna Umahi a lokacin ya na hannu.
El-Rufai ya nemi afuwar jama'a
Kwanaki aka ji Gwamna Nasir El-Rufai yana cewa ya na tsoron ranar da zai tsaya a gaban Allah, a nemi ya fadi abin da ya yi domin tsare talakawansa.
Gwamna El-Rufai ya ce don haka dole ya roƙi gafara da afuwar talakawan Kaduna. Bayan an kai hari a Giwa, Malam El-Rufai ya ce ba ya iya yin bacci.
Asali: Legit.ng