Tsohon hadimin Sule Lamiɗo da wasu jiga-jigan PDP sun bi sahun Kwankwaso zuwa NNPP
- Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta samu karin mambobin PDP a jihar Jigawa, waɗan da suka sauya sheƙa zuwa cikinta
- Tsohon hadimin tsohon gwamna Sule Lamiɗo, Lawan Kazaure, shi ya jagoranci masu sauya sheƙar zuwa sabuwar jam'iyya
- Bayan haka, shugaban rikon kwarya ya mika sakatariyar jam'iyya ga sabbin shugabanni da aka zaɓa
Jigawa - Jam'iyyar NNPP reshen jihar Jigawa maƙwafciyar jihar Kano ta karɓi sabbin mambobin da suka sauya sheƙa daga PDP zuwa cikinta a faɗin jihar.
Da yake jawabi a madadin waɗanda suka sauya sheƙa, tsohon babban mai taimaka wa tsohon gwamna Sule Lamido kan harkokin midiya, Lawan Kazaure, ga ce sun yi watsi da PDP ne saboda wasu dalilai.
Daily Trust ta rahoto cewa da yake zayyana dalilin da yasa suka fice daga PDP, Kazaure, yace sun ɗauki matakin tattara kayansu ne saboda jam'iyyar ta gaza tsayawa da kafafuwanta.
Ya ce PDP ta rasa madafa kuma ba ta da wata tsayayyan hanya da ta sa a gaba kuma sun yi iya bakin kokarinsu a gyara amma abu ya ci tura.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kazaure ya ƙara da bayanin cewa sun kira da jawo hankalin jagororin jam'iyya kan a bi hanyar demokaraɗiyya domin sasanta matsaloli amma suka ƙi saurare da kunnen basira.
NNPP ta sayi sabbin shugabanni a Jigawa
Shugaban kwamitin rikon kwarya, Sanata Musa Bako Aujara, da yake tsokaci yayin miƙa Sakatariyar NNPP ga sabbin shugabanni, ya ce an bayyana waɗan da suka yi nasara ne ta hanyar sahihin zaɓe.
Ya yi iƙirarin cewa jam'iyyar NNPP ta kafa tsari mai kyau a jihar Jigawa, ta yanda za'a iya cewa ta shirya tsaf wajen kwace mulki daga hannun APC a babban zaɓen 2023.
A wani labarin kuma Ministan Buhari a ayyana shiga tseren kujerar gwamna a zaɓen 2023, ya yi alƙawarin ba zai ci amana ba
Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na ƙasa, Abubakar Malami, ya ayyana shiga tseren kujerar gwamnan jihar Kebbi.
Ministan wanda ya faɗi kudirinsa a gaban taron magoya bayansa, ya ɗauki alƙawarin cewa ba zai ci amana ba.
Asali: Legit.ng