Obasanjo ya fadawa ‘Yan Najeriya su kauracewa zaben Atiku, Tambuwal, Saraki da Obi

Obasanjo ya fadawa ‘Yan Najeriya su kauracewa zaben Atiku, Tambuwal, Saraki da Obi

  • Tsohon shugaban Najeriya ya gabatar da jawabi na musamman a wajen bikin Fasto Itua Ighodalo
  • An taya Itua Ighodalo murnar cika shekara 61, don haka aka kira Olusegun Obasanjo ya yi magana
  • Olusegun Obasanjo ya yi kaca-kaca da ‘yan siyasan da ke cewa wasu sun saya masu fam din takara

Lagos - Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya nemi ‘yan Najeriya su raba kansu da zaben masu neman takarar da suke yi wa jama’a karya.

Daily Trust ta rahoto Olusegun Obasanjo yana mai kira ga al’umma su guji kada kuri’a ga duk wanda ke da'awar wasu suka saya masa fam din takara.

Daga cikin masu neman kujerar shugaban kasa da suka yi ikirarin masoya ne suka kawo masa fam din shiga takara akwai Alhaji Atiku Abubakar na PDP.

Kara karanta wannan

Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu, Jigo a majalisar wakilai

Rahoton ya ce sauran wanda ke takamar kyauta aka kawo masu fam sun hada da gwamnan Sokoto, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal da Peter Obi.

Akwai mai girma gwamnan Ribas, Nyesom Wike da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki. Kudin dukkansu bai yi ciwo wajen shiga takara ba.

Wazirin Adamawa ya rike kujerar tsohon mataimakin shugaban kasa a gwamnatin PDP, daga baya ya samu sabani da mai gidansa kafin a shirya a 2019.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Obasanjo
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Obasanjo ya gabatar da jawabi a Legas

Obasanjo ya bayyana haka da yake jawabi a wajen bikin da aka shirya a kan rawan da jagororin kirista suka taka sa’ilin da aka samu kai a mawuyacin hali.

An shirya wannan taro na musamman ne domin taya Fasto Itua Ighodalo murnar cika shekara 61. Obasanjo ya na cikin wadanda suka yi jawabi a wajen bikin.

Kara karanta wannan

N30,000: Sanatan APC Goje ya baiwa matasa da mata sama da 2,000 tallafin dogaro da kai

A cewar Obasanjo, babbar matsalar kasar nan ita ce shugabanci, ya ce kwararrun masana aka dauko kafin a tsara kundin tsarin mulkin da ake amfani da shi.

Da za a samu shugabannin kwarai, da duk komai zai dawo daidai a ganin Obasanjo. Dattijon ya ce duk mai cewa kyauta aka kawo masa fam, ba abin yarda ba ne.

“Yau ana biyan N40m. Wasunsu (‘yan takara) su na cewa matasa ne suka saya masu. Kai! duk wanda ya fada maku wannan karya yake yi, ka da ku zabe shi.”
“Wasu matasan su ka tara N40m? Idan za ku saye fam, ku saya ku fada mana. Babu dalilin yi mana karya.” - Olusegun Obasanjo

PDP da zaben 2023

Dazu aka ji cewa wasu ‘yan jam’iyyar PDP sun samu rabuwar kai a kan wa ya fi dacewa ya rike tutar shugaban kasa tsakanin Arewa da kudu a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Tinubu ya soke taron 'Birthday' dinsa don nuna jimamin harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Atiku, Saraki da Tambuwal sun ce a bar kofa a bude tun da rabon ‘dan Arewa da yi mulki a PDP tun 2010, amma irinsu Nyesom Wike sun ce sam ba haka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng