Gardamar yankin da za a ba takarar shugaban kasa a zaben 2023 ya kawo rigima a PDP

Gardamar yankin da za a ba takarar shugaban kasa a zaben 2023 ya kawo rigima a PDP

  • Kwamitin rabon kujerun siyasa na jam’iyyar PDP ya na daf da gabatar da rahoton aikin da aka ba shi
  • Akwai masu ganin dole ‘dan takarar PDP ya fito daga Kudu, wasu su na da akasin wannan ra’ayi
  • Kungiyar Justice and Equity Group (JEG) ta ba kwamitin shawara a ba kowa damar ya shiga takara

Abuja – The Nation ta ce rikicin da ake yi a game da yankin da za a ba takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP ya na kara kamari a halin yanzu.

Maganar da ake yi ita ce hankali ya koma ga kwamitin kason mukamai na jam’iyyar PDP da Mai girma gwamnan Benuwai, Samuel Ortom yake jagoranta.

Ra’ayin manyan ‘ya ‘yan jam’iyyar hamayya ta PDP ya raba biyu a kan yankin da za a kai tikiti.

Kara karanta wannan

APC ta yi babban rashi yayin da masu biyayya ga ministocin Buhari suka sanar da ficewarsu daga jam’iyyar

Wasu su na cewa a bar ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 ya fito daga kudancin Najeriya. Wasu kuma su na ganin a bar kofa a bude ga kowane yanki.

Justice and Equity Group ta kawo shawara

A makon nan wata kungiya mai suna Justice and Equity Group (JEG) ta rubutawa kwamitin Ortom takarda ta na bada shawarar a bar kowa ya nemi tikiti.

Takardar da Ahmed Muhktar, Yemi Arokodare da Chima Ndugbu suka sa wa hannu ta ce bai kamata PDP ta yi kuskuren kai takarar zuwa wani bangare ba.

Rigima a PDP
Atiku Abubakar da Nyesom Wike Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

'Yan siyasan Arewa sun hakikance

Legit.ng Hausa ta fahimci a gefe guda akwai akalla mutum hudu masu neman takarar shugaban kasa daga Arewa, su na ganin bai kamata a hana su takara ba.

Kara karanta wannan

Jerin shugabannin da suka yi nasara, da wadanda suka sha kasa a zaben jam’iyyar APC

Uku cikin masu neman tikitin yin takarar shugaban kasan da suka fito daga Arewa sun yi takara a 2019, inda Atiku Abubakar ne ya lashe zaben fitar da gwani.

Wike da su Anyim sun ja daga

Mataimakin shugaban kwamitin, Bode George ya na cikin wadanda ba su so mulki ya koma Arewa. Gwamna Nyesom Wike yana da irin wannan ra’ayi.

‘Yan siyasan Kudu da ke neman tuta su ne; Nyesom Wike; Anyim Pius Anyim; Dele Momodu; Sam Ohuabunwa; Nwachukwu Anakwenze da wata Diana Oliver.

Kwamiti ya kusa gama aiki

Rahoton ya ce a ranar 7 ga watan Afrilu kwamitin Ortom mai mutum 37 zai gabatar da rahoton aikinsa gaban uwar jam’iyya domin a dabbaka matsayar a zabe.

Kwanaki Gwamna Samuel Ortom ya yi alkawarin za su fitar da matsayar da za ta gamsar da duk wasu masu ruwa da tsaki ba tare da an samu wani sabani ba.

Kara karanta wannan

Masu neman mulkin Najeriya a PDP sun karu, Gwamnan Ribas ya shirya gwabzawa

Saraki sun janye takara?

Dazu an aka ji maganar cewa manyan ‘yan takarar PDP sun sallamawa Atiku Abubakar ba gaskiya ba ne. Har yau ba a tsaida wanda 'yan Arewa ke goyon-baya.

Osaro Onaiwu ya ce har yanzu Bukola Saraki, Aminu Tambuwal da Bala Mohammed duk su na takara, akasin rahotannin da ke yawo cewa sun hakura sun janye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng