Da Dumi-Dumi: Gwamna Buni ya miƙa ragamar jam'iyyar APC hannun sabon shugaba na ƙasa
- Gwamna Mala Buni na jihar Yobe ya kammala aikinsa ya mika ragamar tafiyar da APC hannun sabon shugaba
- Sanata Abdullahi Adamu, ya karɓi jagorancin APC a Sakatariyar jam'iyya ta ƙasa ranar Laraba, 30 ga watan Maris, 2022
- An gudanar da kwaryq-kwaryan biki ne a gaban gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello da sauran mambobin kwamitin NWC
Abuja - Sabon shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya karbi jagorancin jam'iyya ta ƙasa daga hannun shugaban riko.
Shugaban kwamitin rikon kwarya da shirya babban taro kuma gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya damƙa ragamar APC a hannun Adamu a hukumance.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da jam'iyyar mai mulkin ƙasar nan ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta Twitter.
Hakan ya kawo ƙarshen tsawon watanni 21 da Buni ya jagoranci APC tun bayan naɗa shi shugaban kwamitin riko.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Taron miƙa ragamar jagorancin jam'iyya ya gudana ne a babban ɗakin taro na kwamitin NWC dake Sakatariyar APC ta ƙasa a babban birnin tarayya Abuja.
APC ta rubuta a shafinta cewa:
"Sabon shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya karbi kayayyakin ofishinsa daga hannun shugaba mai barin gado kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni a Sakatariyar jam'iyya dake Abuja."
An zabi sabon kwamitin jagoranci NWC karkashin jagorancin Sanata Adamu ne ranar Asabar, 26 ga watan Maris, 2022 a wurin babban taron APC na ƙasa.
Sabon shugaba ya yi jawabi
Sanata Adamu ya saki jawabi a shafinsa na dandalin Twitter yayin da ya tura Hotunan taron miƙa masa ragamar mulkin APC.
Ya ce:
"A wurin karɓan ragama a hukumance yau, shugaba mai barin gado, Mala Buni ya mana fatan Alkairi. Mun yi wa mutane alƙawari cewa da zaran mun fara aiki jam'iyyar mu zata shiga mataki na gaba."
A wani labarin kuma Jami'an hukumar EFCC Sun Cafke wani Kasurgumi ɗan Najeriya da Amurka ke nema ruwa a Jallo
Jami'an hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki ta'adi sun yi ram da mutumin ne a karamar hukumar Orlu ta jihar Enugu.
FBI na zargin mutumin mai suna, Emmanuel Dike Chidiebere, da aikata damfara da halasta kuɗin haram a ƙasashen uku.
Asali: Legit.ng