Gwamna Yahaya Bello ya bayyana wanda ya kamata ya gaji Buhari a zaben 2023
- Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya magantu a kan wanda ya kamata ya mallaki tikitin takarar shugaban kasa na APC a zaben 2023
- Bello ya ce jam'iyyar mai mulki na bukatar kwararren dan takara wanda zai dora daga inda Shugaba Buhari ya tsaya
- Mai neman takarar shugaban kasar ya ce kada a yi la'akari da yankin da mutum ya fito idan har ya cancanta
Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, na bukatar dan takarar shugaban kasa wanda zai gyara albarkatun kasar ba tare da la’akari da yankin da ya fito ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 28 ga watan Maris, a wata hira da Channels TV yayin da ake tsaka da kira ga a mika shugabancin ga yankin kudancin Najeriya.
Dalilin rabuwar kan sauran jam'iyyun siyasa: Babu jam'iyyar da ke da uba kamar Buhari, inji Ahmad Lawan
Ya ce:
“Abin da yan Najeriya ke bukata shine kwararren dan takara, jajirtacce, mai tunani da wayo wanda zai gyara kasar ba tare da la’akari da yankin da ya fito ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Mun ga shugabanci bi-da-bi a kasar nan a baya kuma mun ga sakamakon shi. Abun da yan Najeriya ke bukata shine mutumin da zai ba da wannan fatan.”
A cewar shi, kasar na bukatar shugaban kasa wanda zai hada kan dukka yankin Najeriya sannan ya dora daga inda Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya.
Rahoton ya nakalto Yahaya na cewa:
“Abun da jam’iyyar ke bukata a yanzu shine mutum mai hankali, wayayye kuma matashi wanda zai kwato shugabanci.”
Shugabancin 2023: Okorocha ya ce ya kamata Tinubu ya hakura ya bar masa tikitin APC
A wani labarin, Rochas Okorocha, daya daga cikin masu neman kujerar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a zaben 2023, ya bayyana cewa zai lallashi babban jagoran jam’iyyar, Bola Tinubu domin ya janye masa wajen mallakar tikitin jam’iyyar.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Okorocha ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a wajen babban taron jam’iyyar na kasa da aka yi a Abuja.
Tsohon gwamnan na jihar Imo ya bayyana cewa akwai yiwuwar shi da Tinubu ne za su iya zama manyan yan takara daga yankin kudancin kasar.
Asali: Legit.ng