Babban Hadimin gwamnan Ekiti ya yi murabus daga mukaminsa, ya fice daga jam'iyyar APC

Babban Hadimin gwamnan Ekiti ya yi murabus daga mukaminsa, ya fice daga jam'iyyar APC

  • Yayin da jam'iyyar APC ke shirin babban taro na ƙasa ranar Asabar, babban ƙusan gwamnatin Ekiti ya yi murabus, ya fita daga APC
  • Babban mai taimkawa kan harkokin da suka shafi zaɓe, Olaiya Kupolati, ya tabbatar da komawa jam'iyyar SDP
  • Ya ce ya yanke aje mukaminsa ne domin yin biyayya da kundin dokokin zaɓe saboda zai nemi takara a 2023

Ekiti - Babban mai taimkawa gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti kan al'amuran da suka shafi zaɓe, Mista Olaiya Kupolati, ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa bayan sauka daga muƙaminsa, kusan gwamnatin APC a Ekiti ya sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP.

A wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 23 ga watan Maris, 2022 kuma ya aike wa Sakataren gwamnatin jihar, Kupolati, ya ce zai bar aiki daga ranar 30 ga watan Maris, 2022.

Kara karanta wannan

Majalisun tarayya zasu ɗaukaka kara kan hukuncin goge dokar zaɓe ta Buhari, sun ɗauki wasu matakai

Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi.
Babban Hadimin gwamnan Ekiti ya yi murabus daga mukaminsa, ya fice daga jam'iyyar APC Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kupolati ya ƙara da cewa ya ɗauki wannan matakin ne domin biyayya da kundin zaɓe 2022, wanda ya shinfita dokar cewa duk wani mai rike da muƙami da yake neman takara ya yi murabus.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, bisa haka ya ɗauki matakin aje mukaminsa domin yana da niyyar neman takarar ɗan majalisar dokokin jiha karkashin jam'iyyar SDP.

Wasiƙar ta ce:

"Ni, Kupolati Olaiya, babban mai taimakawa gwamna kan harkokin da suka shafi zaɓe, na yi murabus daga mukamina daga ranar 30 ga watan Maris, 2022."
"Ina mai miƙa tsantsar godiya ta ga mai girma gwamna bisa wannan dama da ya bani na bauta wa nagrtattun mutanen jihar Ekiti."

Tsohon hadimin gwamnan ya koma SDP a hukumance

Da yake sanar da komawa jam'iyyar SDP a gundumarsa Iye Ekiti, Kupolati, ya ce ya yi haka ne domin haɗewa da tsohon gwamna, Segun Oni, wanda ke da kwarewa da gaskiya.

Kara karanta wannan

Sunayen gwamnoni uku da jiga-jigai 34 da zasu yanke wanda PDP zata ba tikitin shugaban ƙasa a 2023

Ya ce:

"A gani na tsohon gwamna Segun Oni, shi ya fi dacewa da mulkin Ekiti bayan gwamna Fayemi a irin wannan lokacin kuma a shirye nake na taimaka masa."
"Tsohon gwamna mutum ne na mutane, mai gaskiya da rikon amana. Ya yi abin a zo a gani lokacin zangon mulkinsa na farko, dan haka ya cancanci samun dama ta biyu."

Daga ƙarshe Mista Kupolati ya bayyana sha'awarsa ta neman takarar mamba a majalisar dokokin jiha mai wakiltar mazaɓar Ilejemeje a zaɓen 2023 dake tafe.

A wani labarin kuma Jam'iyyar APC ta gamu da cikas, Wani babban ƙusa tare da dandazon mambobi sun koma PDP

Jam'iyyar APC mai mulki ta gamu da wani cikas a Kwara yayin da take shirin babban gangamin taro na ƙasa ranar Asabar.

Tsohon ɗan takarar gwamna kuma jigo a APC ya jagoranci dandazon masoya sun koma jam'iyyar PDP mai hamayya.

Kara karanta wannan

2023: Ku tsayar dani takarar shugaban kasa zan lallasa kowa a zabe, Gwamnan Arewa ya roki PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262