Lissafi ya canza: Shugaban kasa ya bada sabon umarni a kan zaben shugabannin jam’iyya

Lissafi ya canza: Shugaban kasa ya bada sabon umarni a kan zaben shugabannin jam’iyya

  • Muhammadu Buhari ya yi zama na musamman da gwamnonin jam’iyyarsa a kan zaben shugabanni
  • Shugaban kasa ya fadawa gwamnonin APC su fito da wadanda duk za su rike kujerun NWC zuwa yau
  • Bayan haka, Buhari ya bada umarni ga jam’iyya ta maidawa duk ‘dan takarar da ya janye kudin fam

Abuja - Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fadawa jam’iyyar APC ta maidawa duk wani ‘dan takara da ya hakura da neman mukami kudinsa.

A ranar Laraba, 23 ga watan Maris 2022, Punch ta rahoto shugaban kasa yana umartar APC ta maidawa wadanda suka janye takara kudin fam da suka biya.

Wasu ‘yan siyasa sun fasa takara, sun yarda su janyewa abokan hamayyarsu. Don haka Muhammadu Buhari ya hana APC taba irin wadannan kudi.

Kara karanta wannan

Ai ga irinta nan: Kalaman ‘Dan takarar Shugaban APC sun yi masa illa, an juya masa baya

Nairaland ta ce shugaban kasar ya bada wannan umarni ne yayin da ya zauna da gwamnonin APC.

A fito da wadanda za a ba mukamai

Haka zalika, Mai girma Buhari ya fadawa gwamnonin jam’iyyarsa da su yi kokari wajen ganin an zabi sababbin shugabannin APC na kasa ta hanyar maslaha.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban Najeriyar ya ba gwamnoninsa nan da sa’o’i 24 su fito da sunayen wadanda ake so su rike duk wasu mukamai na kasa a jam’iyyar APC mai mulki.

Shugaban kasa da 'yan jam’iyyar APC
Masu neman shugabancin APC Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

Hakan yana nufin za a bukaci da dama daga cikin ‘yan takarar su janye, su bar wadanda ake so. Legit.ng ta fahimci hakan zai sa jam’iyyar APC rasa miliyoyi.

“Masu martaba, yayin da kwanaki biyu kurum suka rage mana ayi zabe, ina kira gare ku da ku fito da wadanda za su rike sauran mukaman da suka rage.”

Kara karanta wannan

Abdulaziz Yari: Zan yi amfani da kwarewata ta siyasa na daidaita barakar da ke cikin APC

“Yadda nan da sa’o’i 24 za a samu ‘yan takarar da kai ya hadu a kansu, za a zabe su a taron.” - Buhari.

A jawabinsa, Buhari ya fadawa gwamnonin su nuna kishin jam’iyyarsu domin babban hadari ne a bari jam'iyyar PDP ta sake komawa kan mulki a zaben 2023.

Aikin da suka ragewa APC

Kujerun da ba a cin ma matsaya a kansu ba sun hada da na sakataren gudanarwa, mai ba jam’iyya shawara a kan harkokin shari’a da mataimakan shugaba.

Sai kuma sakataren kudi, sakataren jin dadi da walwalwa, ma’aji, shugabar mata ta jam’iyya, shugaban matasa na kasa, da irinsu jagoran nakasassu.

Mutane 170 za su yi takara

An ji cewa tsohon gwamnan Bauchi da tsohon shugaban majalisar tarayya, da wasu Sanatoci su na neman kujerar mataimakin shugaban jam’iyya a zaben.

Tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari da Hon. Faruk Adamu Aliyu sun birkitawa APC lissafi, sun saye fam duk da an hana yankinsu shiga takara.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni ga masu sukar APC: Taron gangami ne a gabanmu, ba ta kowa muke ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng