Sabon Gwamna ya fara kuka bayan ya iske an bar masa baitul-mali wayam sai uban bashi

Sabon Gwamna ya fara kuka bayan ya iske an bar masa baitul-mali wayam sai uban bashi

  • Charles Chukwuma Soludo ya bayyana abin da ya samu a cikin asusun gwamnatin jihar Anambra
  • Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya ce kudin da ke cikin Baitul malin jihar ba su wuce N400m ba
  • Tsohon gwamnan bankin CBN ya yi alkawari jama’a za su rika sanin abin da ya shigowa jiharsu

Anambra - Sabon gwamnan da aka rantsar a jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo, ya yi bayanin halin da ya iske asusun gwamnatin da ya gada.

Mai girma sabon gwamnan ya yi wannan jawabin a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin nan na Arise TV a ranar Talata, 22 ga watan Maris 2022.

Kamar yadda Premium Times ta kawo rahoto, Farfesa Charles Chukwuma Soludo ya ce ya iske N300m zuwa N400m ne duka-duka a Baitul malin jihar.

Kara karanta wannan

CAN ga El-Rufai: Ka daina wani girman kai, ka amsa ka gaza a fannin tsaro

Amma kuma ya ci karo da bashin kusan Naira biliyan 109 a lokacin da aka rantsar da shi a ofis.

Tattalin arzikin Anambra bai da karfi

Charles Chukwuma Soludo ya koka da cewa tattalin arzikin jihar Anambra bai da karfi, amma ya sha alwashi cewa zai yi kokarin magance wannan matsala.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wajen bashi, tsohon gwamnan na CBN ya shaidawa manema labarai cewa ya samu ana bin jihar Anambra biliyoyin kudi, amma ba a bar abin kirki ba.

Sabon Gwamna
Farfesa Charles Soludo Hoto: CCSoludo
Asali: Twitter

Masanin tattalin arzikin ya nuna sam bai son yin magana a kan yadda Willie Obiano ya damka masa jihar domin Baitul-malin da ya iske abin ban dariya ne.

“Kowa ya san tattalin arzikin jihar bai da karfi sosai, idan za ma ayi adalci kenan. Kudin da mu ka samu a bankuna idan zan tuna kusan N300m zuwa N400m ne.”

Kara karanta wannan

Daga hawa kujerar mulki, sabon Gwamna ya ce zai nada Kwamishinoni nan da kwanaki 7

“Sannan kuma binciken da aka yi daga Disamban 2021 ya nuna bashi ya kai N109bn.” - Soludp.

Za mu yi gyara - Farfesa Soludo

Daily Trust ta rahoto Farfesa Soludo yana cewa gwamnatinsa za ta rika yin abubuwa ke-ke-da-ke-ke wajen kula da asusun al’umma domin tabbatar da gaskiya.

Soludo ya ce zai rika wallafa bayanin halin da tattalin arzikin jihar ke ciki a kai-a kai domin kowa ya san abin da ya shigo Anambra da kuma abin da aka yi da su.

Saraki na neman mulki

An ji cewa tsohon shugaban majalisar dattawa ya yi alkawari zai ba matasa kujerar Ministoci tun da suka sayo masa fam din PDP ba tare da aljihunsa ya yi ciwo ba.

Bukola Saraki ya ce idan ya samu mulki a 2023, to zai ba matasa duk wata kujerar karamar Minista, kuma dole zai rika tafiya da su a harkar gwamnatinsa a PDP.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari da Gwamnoni suka karbo bashin Naira Tiriliyan 6.64tr a cikin shekara daya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng