Daga hawa kujerar mulki, sabon Gwamna ya ce zai nada Kwamishinoni nan da kwanaki 7

Daga hawa kujerar mulki, sabon Gwamna ya ce zai nada Kwamishinoni nan da kwanaki 7

  • A karshen makon nan ne Charles Chukwuma Soludo ya shiga ofis a matsayin Gwamnan jihar Anambra
  • Farfesa Charles Soludo ya bayyana cewa a makon gobe zai fitar da sunayen sababbin Kwamishononi
  • Sabon Gwamnan ya shiga ofis, har ya fara zama da jami’an tsaro da sakatarorin gwamnati tun a jiya

Anambra - A ranar Alhamis, 17 ga watan Maris 2022, aka rantsar da Farfesa Charles Chukwuma Soludo a matsayin sabon gwamna a jihar Anambra.

Charles Chukwuma Soludo ya bada sanarwar cewa zai nada wadanda za su rike masa kujerar kwamishononi a gwamnatinsa nan da kwanaki bakwai.

Tsohon gwamnan babban bankin CBN ya yi wannan bayani ne yayin da ya ke jawabinsa na farko bayan rantsar da shi a kan kujerar gwamnan Anambra.

Punch ta ce an yi bikin rantsar da sabon gwamnan ne a garin Agu-Awka, Awka, jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Kwastam Ta Kama Motar Ɗangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250

Charles Chukwuma Soludo ya shaidawa mutanensa cewa ba zai bata wani lokaci ba, nan ta ke zai shiga yin aiki domin cika alkawuran da ya yi wa al’umma.

Rahotanni sun ce har Farfesan ya nada wadanda za su rike masa manyan mukamai. Nan da makon gobe majalisar jihar za ta samu sunayen kwamishinoni.

Sabon Gwamnan Anambra
Charles Chukwuma Soludo Hoto: www.lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Na soma aiki tun yanzu

“Wannan ce ranar farko na a ofis. Na riga na shiga bakin aiki, kuma zan yi aiki na akalla sa’o’i takwas a kowace rana.”
“Mun samu tsawon fiye da wata daya tun da mu ka samu gagarumar nasara a zabe. Yanzu lokaci ne da za mu soma aiki.”
“Ba mu da sisi ko kobon da za mu kashe wajen sharholiya. Nan da ‘yan mintuna zan nada manyan jami’an gwamnati.”

Kara karanta wannan

Anambra: Laifuka 3 da suka jawo aka kama tsohon gwamna Obinao garin tserewa Amurka

“Zan fara da kiran taron majalisar tsaro, daga nan in gana da sakatororin din-din, sai taro da Okpoko da kusoshin gwamnatina.”
“Nan da mako mai zuwa, za a aika da jerin sunayen kwamishinoni zuwa gaban majalisar dokokin jiha.” - Charles Soludo.

Fadan Bianca Ojukwu da Ebelechukwu Obiano

Dazu kun samu karin bayani a game da abin da ya jawo rikici ya barke tsakanin Ebelechukwu Obiano da Bianca Ojukwu wajen nada sabon gwamna.

Wadannan manyan mata biyu sun kicime da fada yayin da abin ya kai ga mari a lokacin da ake rantsar da Charles Soludo a matsayin sabon gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng